P70

1.5K 89 1
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated to my sister Khadeeja Usman Allah ya bar min ke._

*Bismillahir rahmanir raheem*

_A good heart and a good nature are two different issues, A good heart can win many relationships, But a good nature can win many good hearts._

🅿 *70*

Kwanan Fateemah biyu agidan sannan ta 'dan saki jikinta, Daddyn Abuja ma daya dawo sosai yayi farin ciki da zuwanta dan ko shima bawani da'di yaji da barinta da akayi acan ba kawai de yayi shiru ne saboda al'amarin ahannun matan yake, yanzu kuwa da ya ganta ya kuma ji labarin cewa Abbas ne ya kawo ta ai shikenan gaba 'daya sai ya manta ma da haushin Abbas 'din daya keji ya ringa sa masa albarka.

'Ko'kari sosai Hannah keyi wajen ganin ta mantar da Teemahn damuwar da take ciki, saboda bata barinta zama shiru sai de in tatafi makaranta wanda makarantar ma dan ya zama dole ne shiyasa lokuta takance da ita badan tana zaman 'dakin rasuwar mijinta bama da se ta ringa rakata makarantar ai.

Teemah kam baki take ta6ewa ta yi shiru, dama yanzu gaba 'daya ta canja wannan rashin jin duk babu shi ta dawo wata salihar 'karfi da yaji, wani lokaci idan tana abu se kaga kamar ba ita ba.

Haka abinci ma yanzu bata ci da wasa 3square meal 'din nan duk basa wuceta takanyi 'ko'kari taci a'kalla kamar spoon goma koma fi akowani lokacin cin abinci, Ummah sosai take jin da'din canjawar tata musamman data ga yanzu tasaki jiki har tana cin abinci batare da an takurata ba.

Damuwar ma duk ta rage shi yanzu ta barwa zuciyarta, addu'ah kawai take masa akowani lokaci musamman idan tayi sallah toh sosai take 6ata lokaci waken yi masa addu'ah wanda a lokacin ne tafiya yin kuka sai de ko Hannah bata bari ta fahimci yanayin data ke shiga.

Tana waya dasu mummy da Anty akai-akai, inda mummy kanta da taji cewar Teemah ta dawo Abuja sai da ta sau'ke ajiyan zuciya da can 'din ma kawai ta daure ranta ne tare da yiwa Anty kawaici, amma tunda ta koma Dubai sai taji zuciyarta ya kasa nutsuwa sai take ganin kamar Antyn zata iya sake cutar da Fateemah tunda tana gabanta.

Anty kuwa bayan tafiyar Teemah da kwana biyu sai taji damuwarta ta dawo mata sabo fil, tunaninta ya yawaita akoda yaushe bata da aiki sai zubda 'kwalla, gashi babu wanda ke zuwa gurinta ayanzun, Abbah ma  'kara nisanta kansa yayi da ita, dan tun tafiyar Teemah sau 'daya kawai ta ganshi, wannan 'dinma ta window ne lokacin shigowar sa gida kenan jin dirin mota yasa ta le'ka sai taganshi.

Ganin sa 'din kuma sai ya 'kara kashe mata zuciyar dan gaba 'daya Abbah ya lalace wani rama taga yayi na masifa, tausayinsa har se da ya sata sakin hawaye, tasan koma menene yafaru laifinta ne, mutuwa ba a hannunta yake ba, amma tasan son zuciyarta shine sanadin komai.

Komawa tayi ta jinginu da jikin window ta lumshe idanu yayinda hawaye suka ci gaba da gangarowa ta 'kasan idanun suna sau'ka saman kuncinta, samata 'daga kanta tace
" _Allah na tuba ka yafe min, ka yafe min kura kuraina, ya ubangiji Allah ka sanyaya zu'katan duk wa'danda na_ ' _kuntatawa, Ya Allah kaji'kan Mahmud ka haskaka masa 'kabarin sa_ "

Washe gari da sassafe tayiwa 'dakin Abbah tsinke, sallamrta ka'dai ya amsa saboda darajar da sallama ke da shi ga dukkan wani musulmi, daga nan yaci gaba da shirinsa be ko kalli inda take ba, kallo 'daya Anty tayi masa ta fahimci cewa shirin tafiya yakeyi dan haka sai ta zauna agefen gado ahankali tace " barka da warhaka Alhaji fatan antshi lafiya"

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now