P63

1.3K 78 6
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*


*Bismillahir rahmanir raheem*

_Beauty catches the attention but character catches the heart........_

🅿 *63*

Tausayin ta ne yakama shi dan yasan kamar yanda bakinta ya furta hakan toh ko cikin zuciyarta ma hakan ne, kuma duk wanda yace ma yanasan 'da toh yana so 'dinne da dukkan zuciyarsa, saboda soyayyar 'ya'ya 'ka'k'karfar soyayya ce dake wanzuwa azu'kanta dukkan iyaye.

Juyawa yayi gaba 'daya ya fuskance ta sai ta fara 'ko'karin guduwa daga inda yake.

Hannu Mahmud yasa ya dawo da ita inda take zaunen sai tayi maza ta me da kanta 'kasa yanda baze ga fuskarta ba, 'kafafunsa dake tan'kwashe ta kifa kanta akai tana murmushi, hannunta kuwa ri'ke acikin nasa.

Hakan kuwa datayi sai yasa Mahmud baya ganin komai sai bayanta.

Shima murmushin ne ya kubce masa yana murza yatsunta dake hannunsa yace mata
" _kinsan cewa abin kunya ne meyasa dama kika fa'da_ ?

Luf tayi ta'kiyin ko motsi kamar ma bada ita yake maganar ba illah murmushin data keyi 'kasa-'kasa.

Kunyan iyayin nata ba karamin birge shi yake yi ba, aransa ya yanke shawaran gara kawai ya gaya mata gaskiyan abinda ke faruwa dashi tunkan shirun nashi ya 'kurewa ha'kurinta.

Mahmud jan jikinsa yayi ya jinginu da jikin gadon ya lan 'kwashe hannunsa akan 'kirjinsa tare da mi'kar da 'kafafunsa wanda hakan yabawa Fateemah daman kwantar da kanta da kyau akan 'kafafun nasa tana kallon gefe, har yanzu ta'ki ta kalli inda yake ma balle har su ha'da idanu dashi ita adole kunya takeji.

Mahmud ne yafara magana da fa'din

" _Fateemah kinsan kwanan nan nayi tafiya ko_ ?

Shiru tayi masa taki yin magana, shima yasan bazata tanka sa ba dan haka sai yaci gaba da maganarsa.

" _Daga Umar abokina babu wanda yasan dalilin tafiyar danayi wacce nayi ta ne dan neman magani wa matsalar data same ni da ni kaina bansan_ _takamamman lokacin da hakan ya faru ba, daga zuciyata sai Umar sai kuma ke da zan sanar dake ayanzun bayaga haka babu wanda yasan abinda ke damuna. Fateemah ada na kasance mutun ne ni lafiyayye ta ko wani 6angare wanda ni kaina na shaidi hakan bana bu'katar sai nayi_ _wani dogon nazari akan haka, dai-dai da rana 'daya ban ta6a tsintar kaina cikin wata matsala_  _acikin jikina ba, wanda badan nasan hakan ba da babu abinda zai sa in amince da batun auranki, bama ke ba koda kuwa wata_ _macece daban bazan taba yadda in aureta ba ko dan gudun kar na shiga hakkinta_ _ma_ .
_Kwatsam bayan aure na dake sai na  tsinci kaina cikin wani hali, halin da baze ta6a barina in rayu da iyalina cikin kwanciyar hankali ba, nakan gode Allah amafi yawancin lokuta daya sanya kece kika kasance mata agareni ba wata daban ba, wanda na tabbata da wata daban ce da yanzu mun da'de da samun matsala da ita ko ma mun_ _rabu, saboda ba kowacce mace bace zata iya zama dani ahaka yanayin da nake mu zauna cikin rufin asiri ba sai ko in nayi sa'a_ , _kinga ke kuwa kin zauna dani ahakan baki ta6a nuna min damuwarki akan haka ba baki ta6a_ _nuna min_ _gazawarki ko canjin fuska akan zama dani ba duk da nasan ba asan ranki bane, ni da kaina_ _nasan kina da bukatar kasancewa da mijinki alokuta da dama ba sai an_ _sanar dani ba ni ni shaida ne akan wannan.Fateema_
_kinga ko awannan 6angaren ma ka'dai dole in godewa Allah na tare da yabawa da za6in_ _Abbah na, domin shi yayi ruwa yayi tsaki wajen ganin kin kasance mata agareni. Ko_ _yanzun ma banyi mamaki ba dan kince kinada bu'katun baby_ _domin nasan wannan shine burin dukkan ma'aurata, ni kaina Fateemah inason baby amma_ _ayanayin dana tsinci kaina kinga dole ne na ha'kura na sanyawa_ _zuciyata salama har zuwa lokacin da Allah ya bani lafiya inda rabona sai kiga yabani"_

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now