P91

3K 150 32
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated 2_
*Maman Ahmad &*
*Anty Maimounath o.g ( Mahnoor).*
*Mungode da 'kaunar da kuke nuna mana Allah Ubangiji ya bar mana ku (Ameeen)*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

  _U can’t change what happened in ur past, so b4 u let it destroy ur future, learn to live with it...._

🅿 *91*

Ganin kamar zata 6ata mai lokaci ne sai yayi hanzarin wucewa da kansa ya za6o mata doguwar riga da hijab.

Da taimakon sa ta sanya kayan a jikin ta tare da rufawa kanta hijab 'din still tana zubda hawaye suka fita zuwa clinic dake cikin  barrack 'din nasu.

Daya ke ma koda wani lokaci kaje suna aiki basa yankewa so ba tare da wata damuwa ba  suka isa ga babban Doctor 'din dake kan aiki a lokacin.

Abbas da kansa ya yiwa Doctor bayanin abinda ya kawo su Teemah kam sai hawaye take tana faman rarraba musu idanu daga gefe.

Wata nurse likitan ya 'kira yayi mata bayanin abinda zatayi sannan ya ha'da su da Teemah suka je ta 'dibi jinin ta sannan ta bata wani 'dan k'aramin abu tasa ta yin fitsari a ciki.

Teemah kam duk da tana cikin wani yanayi na tsananin damuwa amma hakan bai hanata ta6e baki da " mitar wai banda 'kazanta to me ze sa ta haka, a hakan ne wai Yayah zai ce itama ta zama likita" sake kallon robar tayi tana sake jinjina rashin kunya da 'kazanta irin ta likita.

Zuwa tayi ta mi'ka ma Nurse 'din tana sake kallon 'kwayar idanun ta amma sai taga bata wani nuna komai ba ta kar6a ta wuce laboratory da shi, bin bayan ta Teemah tayi da idanu har ta 6acewa ganin ta, ita kam wurin tap taje ta ringa dirzan hannun ta kamar zata sille shi sai da ta tabbatar ya wanku tas sannan ta bari ta koma office inda ta baro shi.

Zaune ta same shi shika'dai yana amsa waya ga dukkan alamu Doctor 'din ma ya fita ne.
      A hankali ta 'karasa jikin sa ta zauna tayi luf, sai da ya kammala da wayar kafin ya tambaye ta har an gama ne kai ta 'daga masa tare da fa'din " Yayah wurin ma zafi yake min sosai"
Tayi maganar tare da nuna masa gurbin da aka ja jinin.
Hannu Abbas ya kai yana shafa mata a hankali yace " Vry sorry...zai daina zafin ai kinji"
Cikin sakalci da marairaita ta d'age kanta sama tare da fa'din  " har da fitsarina fa ta kar6a Yayah".
   Abbas duban fuskar ta yayi sannan ya ce mata " ba komai ai test za'a yi da shi".
    Sai ya kai hannu jikin ta ya ta6a yanayin zafin jikin sannan ya 'kara da fa'din " har yanzu cikin na miki motsin ne?"
  Teemah sai tace " Ah'ah.......ya daina amma Yayah ni tsoro nake ji"

Taran ta yayi da fa'din " Nima inajin hakan Zahra.. but Doctor yace min 'kila abin alkhairi ne zai same mu, amma bari dai mu jira ganin result 'din ko sai muga ko menene?"

Teemah sai ta 'daga kai alamar "to" tayi luf a jikin sa amma abin sai yana bata mamaki, kasa jurewa tayi sai 'dago tare da sake fa'din " Yayah dama akwai alkhairi a cuta ne?"
   Abbas sai yayi murmushi sannana yace " akwai mana Zahra komai ai da irin 'kaddarar da yake zuwa dashi wani mai kyau wani kuwa akasin haka, inajin tamkar wani gagarumin farin ciki ne zai same ni, i feeel ths in my heart kuma ina fatan hakan ya kasance ki kwanatar da hankalin ki kinji ko insha Allahu ba abin damuwa bane".

CAPTAIN ABBASOnde histórias criam vida. Descubra agora