P38

1.2K 73 1
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍

*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Don’t be ashamed to be different........ Be proud that Almighty Allah made you like no one else.

🅿 *38*

Mummy na can uwar 'dakinta taga daddy ya 'kirata awaya akan wai tafito parlour yanzu yanzun nan.

" lafiya kuwa?"

Ta tambaye shi

Sai yace " lafiyar kenan Khadeeja".

yana gama fad'an haka ya yanke 'kiran sai kwai ta tashi ta fito parlourn domin ams a 'kiran Daddyn.

Sai dai tun kafin ta 'karaso tafara jin zuciyarta na tsinkewa, bata san dalili ba amma sai dole hakan yasa yanayin saurinta ya ragu ba kamar yadda ta farao tafiyan da farko ba.

Koda ta iso parloun ma ciki-ciki tayi sallama bata damu da ko daddyn yaji ko be ji ba domin damuwar luguden da zuciyarta keyi ne ka'dai aganbanta awannan lokacin.

Bata ankara da ko mutune nawa bane zaune a d'akin ba har se da ta iso sannan ta 'daga kai a'ko'karinta na neman inda ya yadace tazauna sai kawai idanunta suka hango mata yah yusuf zaune agefen daddy.

Yatsa ta 'daga tare da fa'dan sunan shi cikin tsananin mamaki

" Yah........... Yusuf.........kaine ko............ko.........i"adanuna ne...?

Murmushi yayi mata sannan yace " Nine nan ba idanunki bane Khadija 'Karaso ki zauna".

Ya 'karasa maganar tare da nuna mata wajen zama.

Bata 'karaso inda yake 'din ba sai zune jagwab a inda take tsayen tama kallon shi yayinda idanunta suka da'de da fara zubda ruwan hawaye.....

" Ashe zan sake ganin 'dan uwana aduniya........ashe da rabon in sake ganin ka, Yah Yusuf me yasa ka manta dani, kamanta da koni wacece agareka...ka manta da............

Daidai nan daddy ya dakatar da ita da fad'in " Khadija " !

Da 'karfi yayi maganar wanda yasa dan dolenta tayi shiru sai dai hawayenta dasuka kasa tsayuwa.

Teema ce ta taho da niytan zuwa gurin mummyn ta ta sai ta tarar dasu a parlour dukkansu shiru sai mummynta dake zaune a'kasa kamar me neman gafara tana kuma share hawaye.

A sukwane ta iso gurin mummyn ta zauna itama kusa da ita tafara tayata goge hawayen batayi magana ba amma ga dukkan alamu kukan take shirinyi itama.

Daddy da yaga haka sai ya 'kirata akan tazo wurinshi sai kawai ta kalleshi batare da tayi niyyan tashi daga jikin mummyn ba tace

" daddy me yasami mummy"?

Rashin sanin abin da zai ce da ita yasa shi yin shiru " toh me ze mata yasaka mahaifiyarta kuka?".

Juyawa yayi ya kalli Yah yusuf instead of ya bata amsar tambayar da tayi masa, cikin sa'a kuma daidai nan mummy ta dakatar da kukanta ta kamo Teemah, ta rungumeta ajikinta, tana 'dan bubbuga bayanta.

Daddy da yah yusuf ne suka ha'da baki wajen bawa mummy ha'kuri.

Sai tace bakomai ai ya wuce tunda taganshi yanzu, tace abinda yasa ma har yaga tana kukan bakonai ba ne face tunawa da tayi da Mahaifansu, ta tuna irin gwagwarmayan da mahaifinsu yasha arayuwa 'karshe kuma Allah ya kar6i abinsa, daga baya kuma mahaifiyarsu,  wacce tayi iyah 'ko'karin ta wajen ganin ta kula da rayuwarsu yanda ya kama ta bayan ba ran mahaifinsu amma ita ma Allah ya kar6i ranta tun ba aje ko'ina ba.

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now