P9

1.6K 102 0
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

Dedicated
2
*Safiyyah Aliyu* *Wakili* . &
*Khadija candy*
I heart u guys tnx 4 ur luv nd suppoart_ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

A Mistake increases your experience & experience decreases your mistakes. You learn from your *mistakes* and then others learn from your *success* .👌🏻

🅿 *9*

Zama tayi abakin gadonta daga ita sai pant da bra ranta amatuk'ar 6ace,asama take jin ran nata,"wai wannan shine yah Abbas d'ina kuwa anyah?

"Ayanda mummy take fad'a min ai yah Abbas baya min mugunta,amma shi wannan daga zuwansa gidanmu har ya iyah bayyana nashi salon muguntar,kamar fah yasan abinda nafi tsana kenan arayuwa ta wannan jan kunnan,don ko mummy duk ranar da ta min ma wuni nake bana kulata,shiyasa ma ban fiyah yin abinda nasan zai sa ta min irin hakan ba,sosai nake kiyayewa,Ai kuwa da daddy zan had'a shi ya ramamin abuna.

Murmushi ne ya kwace mata dalilin tunowa datayi da sanda daddy ke jan kunnansa,
"Allah shi kara"

Tace afili.harda cije bakinta irin na muguntan nan.

Daga nan ta ta shi ta nemi kaya tasaka sannan ta fito tasamu Mummy da Baabah Lami a kitchen ko kulasu ba tayi ba,ita adole fishi take yi an mata ba daidai ba,mummy ma ko inda take bata kallah ba,Sai Baabah Lami ce ma tayi mata magana,ita ma maganar tata k'ara 6ata ran Teemahn yayi, dan cemata tayi
"Fatun daddy ya akayi ne naga kinata shan k'anshi haka?

Bata kulata ba sai baki data k'ara turowa,dan ta tsani wannan sunan wai

"Fatu,"

Fuuu......ta juya tafice daga kitchen d'in aikin da batayi ba kenan,daman mummy ce tace matuk'ar tana gida lokacin yin girki yayi toh dole ne tashiga kitchen d'in ayi da itah,shiyasa yanzun ma ta zo,toh amma tun kan ma takama aikin Baabah Lami ta kunnata dayake daman a 90 take,kuma dama tun asali ta tsani "fatun" nan, abakin Baabah Lami kad'ai tafara jinsa
kuma suna yawan shan rigima da baabah Lami d'in akan sunan,kwanaki harta da'n daina fad'ar sunan sai gashi kuma shi yau kuma ta tuno dashi,kawai sai ta fake da hakan  k'ara gaba abinta,dama ba son yin girkin takeyi ba tsoron mummy yasa tafito.

Murmushi mummyn tayiwa Baabah Lami tana kallon fuskar ta tace "kin k'ara rura mana wutar kuma ai inaga"

"Aikuwa dai,naga alama"cewar Baabah Lami d'in tana d'an dariyah.

Mummyn ce ta k'ara da cewa "fushi takeyi wai yanzun da yayanta,amma inaga abin kowa ma bai tsirah ba."

Murmushi sukayi dukkan su,daga nan suka ci gaba da sabgoginsu akitchen d'in suna yi suna d'an ta6a hira jifa-jifa.

Basu k'ara had'uwa ba sai bayan isha'i,dasuka zo cin abincin dare,Nan ma mummy tace taje maza tak'ira shi.

Tana jin abinda mummy tafa'da ta fara bubbuga k'afafu ak'asa,tana fad'in "haba mummy shi wai bazai zo da kansa ba sai ank'irasa"?

Tsawa mummy ta daka mata "bana son rashin kunyah Teemah,aiken nawa ne bazaki ba ko kuwa shid'inne kika fi k'arfin ki k'irashi"

Tana jin haka ta juya ta fara tafiyah zuwa d'akin nasa,

"mthww" mummy taja tsaki biyan tajuya d'in, ita kuwa haushi kamar ya kasheta sai mita takeyi k'asa-k'asa ahankali "wlh mummy duk so take yi ta zubar min da ajina agun wannan mutumin😅,so take ya raina ni gaba d'aya.(kujimin yarinya fah🤔😏)

Bakinta kuwa kamar na 6era tsabar yanda ta turo shi gaba.

Duk da ran mummy a6ace yake,amma bata kasa fahimtar yanayin Teemahn ba,kuma duk tasan bazai wuce akan abinda yafaru d'azun bane,take wannan abun.

Haka taje k'ofar d'akin ta tsaya daga waje tana knock in d'in k'ofar,jitayi babu wanda yace mata ko cikanki ne,sake bugawa tayi da 'dan k'arfi,amma still shiru taji, babu alamun ma anjita.
Hakan yasa ta tura k'ofar azuciye,tashiga cika batare ma da sallama ba.

Gani tayi yanzun d'akin da haske ba kamar d'azu da ta zo ba.

Ta6e baki tayi tare da rarraba idanu ad'akin dan bata ga alamar mutun ba aciki.Komai nakin tsaf dashi tagani,babu gurin data isa ta kushe ad'akin,sai uban k'anshin turarensa mai dad'in shak'a.

Ita kuwa dan iskanci sai ta d'aga hannunta ta toshe hancinta da su,harda ta6a fuska,adole wai turaren bai mata ba ita.

Dai dai shima yabud'e k'ofar d'akin ya shigo,ga mamkinsa sai yaga tana toshe hanci,k'arasa shigowa yayi a mamakance idonsa na kanta,so yake yaji menene dalilinta na toshe hanci a muhallinsa,tunda yasan bai bar komai ad'akin da zai sa har aji wani abu makamancin wari ba,dan ko bayin dake cikin d'akin ma atsaftace yake,ko abinci inta kama sai ka iyah ci aciki,balle ma shi bayaga wanka babu abinda ya had'a sa da bayin tunda yazo gidan sai ko alwala.

Bin d'akin ya sakeyi da kallo akaro na biyu sannan ya kalleta, wuri-wuri tana rarraba idanu,taku yad'anyi kad'an zuwa inda take,tana ganin haka tayi baya itama da sauri,ganin haka sai ya tsaya a inda yake d'in.

"Wani isakanci ne yasaki toshemin hanci ad'aki?"

Dan sosai abin yaba shi haushi,ba k'aramin cin fuska bane yin hakan ga wani,babu wanda zai so ace anji wani abu da ya danganci hakan a inda yake rayuwa,balle mutun irin Abbas da tun tashinsa da tsafta aka sanshi,tun yana yaro ya tsani k'azanta.....................

"Ba tambayarki nakeyi bane"

Ya fad'a atsawace dan jin bata amsa  masa tambayar farkon ba.

Muryarsa na razana ta amma,dan jikinta har rawa ya fara,amma haka ta dake ta bashi amsa da

"d'akin yana wari ne"

Ranshi a6ace yake amma baisan sanda ya zaro idanu waje ba tsabar mamaki,

"Wari kuma.......?
"Warin me toh?
Ya tambayeta.

" *Turare* "
Ta bashi amsa kanta tsaye.

Tsabar takaici kasa yin magana yayi,illah kallon daya bita dashi,amma dai yad'an ji nutsuwa datce warin turare ne,abin takaici kuma har yanzu bata bar toshe hancin ba.

Gani da yayi still tana rufe da hancin ta ai sai ya yunkura zai kamota,tana ganin ya nufota kuwa ta juya baya,dagudu tabar d'akin,cikin sa'a ma abud'e tasamu k'ofar,dan mamakinta ne yasa daya shigo ko k'ofar bai mayar ya rufeta ba,shiyasa tasamu sauk'in gudu,fit ta fice abinta batare da ta tsaya jan k'ofar ba.

Sai da ta tsaya wani lungu ta daidaita numfashinta kafin ta isa wurin mummyn,
"Mummy wai yana zuwa"

"Uhm" mummyn tace sannan ta k'ara. Da fad'in yakin da'de,

"Bansame shi ad'akin bane mummy" tafad'a kamar wata mumina, dan ji take ranta wasai yanzu dalilin wannan abin data yimasan.

Shikuwa bayan fitar ta ad'akin sai yaje ya tura k'ofar tare da fad'in "useless kawai" sanin da yayi wa kansa, k'anshi ko wari ko yaya suke kuwa sai ya jiyosu indai wad'annan abubuwan ne,bata isa ta nuna masa jinsu ba.

Dawo wa yayi cikin d'akin yatsaya ya sake k'arewa ilahirin d'akin kallo,sai kuma yayi murmushi,
"zan had'u da ke ne yarinya"
afili ya fad'i hakan sannan ya ka'rasa bakin gado ya ajiye wayarsa.

Shima ya zauna ya fara 6alle botiran rigarsa,
har ya kusan 6allewa sai kuma ya tuna k'ila aikota akayi,
tunda yanzu lokacin cin abincine agidan kamar yadda yasani tun ada,
take sai ya mik'e ya fice daga da'kin.
Ya nufi main parlour.................


Drop ur comment pls readers🤞🏻,inkuna son ku faranta min🙈

*Salmerhn* 😍 ku ce 👌🏻

CAPTAIN ABBASTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang