💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
_Treat your parents with loving care. You will only know their value when you see their empty chair._
🅿 *50*
Abu'de yasamu 'kofar dan haka kanshi tsaye ya tura kansa ciki ya shiga, sai de yana shiga ya tsaya daga bakin 'kofar dan ganin mutane biyu ne acikin 'dakin.
Dubansa ya kai kan gado domin ya banbancewa idanunsa cikin su biyu amma tunkan tunaninsa yayi nisa yafara jiyo muryar wacce ke kwance akan agadon kunnan ta sa'kale da earpiece tana bin bakin wa'kar Umar m Shareef mai taken ( SAQAR ZUCI) ,hakan yasa yayi saurin fahimtar cewa wannan wata dabance bawacce yasani ba, 'dauke idanunsa yayi yah mayar wajen mirror inda ya hango wata kuma azaune amma kallo 'daya yai mata ya gane ko wacece ita, domin yasanta da san zama gaban dressing mirror, dan haka sai ya 'daga 'kafafunsa cikin nutsuwa ya isa gareta.
Zaune take tayi zugum tun 'dazu tana kallon kanta acikin mirror 'din, sai de azahiri ba ganin kan nata take ba, tunani kawai takeyi da bata san inda ya dosa ba.
Dukkan su basu lura dashi ba yanzun, dan ita wancen wayar datake sarrafawa ahannunta shiya dauke mata idanu yayin da ita kuma wannan hankalinta yatafi ga tunani, kuma ma a yadda ya shigo 'din ba lallai ne kasani ba koda kuwa kana daidai cikin hankalinka, ne dan tamkar wani marar gaskiya haka ya shigo ballantana su da kowa hankalinsa yana wani wuri ne daban.
Da isar sa kusa da itan sai ya tsaya daga bayanta shima yana kallon fuskarta ta cikin madubin gani yayi ta yi kyau sosai fiye da ganinta dayayi na 'karshe, hakama ramarta ta 'dan zarta yanda ya ganta last week.Dubansa yakai ga hannayenta yaga yadda hannayen suka sha kyau cikin zanan flower baki da ja kamar kar su rabu da hannun nata sukasance haka har abada.
" is it all because of th...............!
" ohh no bahaka bane"!
Ya fa'da tare da jijjiga kansa.Be da'de da tsayuwa awurin ba sai ta mi'ke tsaye sanadiyyan tuno maganar Ummah datayi akan ruwan wankan da aka ha'da mata tun 'dazun mai cike da ha'din kayan 'kamshi musamman aka ha'da saboda ita inda Ummahn tace mata karta kuskura ta bari ruwan ya huce batare da tayi wankan ba domin da 'duminsa akeso tayi wanka saboda zaifi kama jikinta yanda akeso idanta gama kuma me shiryata zata zo "
tunowa da wannan maganar ne yasata ta mi'ke tsaye da 'dan sauri domin cika umarnin Ummahn.Amma mi'kewanta keda wuya sai ta hango mutun tsaye daga gefenta yana kallon ta, bata waiwaya baya ba sai kawai ta kalli fuskarsa ta cikin madubin tayi murmushi, jikinsa sanye yake cikin kaftan mint green 'dinkin ba 'karamin kar6ar sa yayi ba, rigar tsayinta be wuce gwiwarsa ba, hannun rigar 'daure da links, irin 'dinkin dayafi birgeta kenan acikin 'dinkun maza, yasanya hula wacce ta dace da kalan kayan jikin nasa.
Hannu ta 'dago ta nufi madubin dashi daniyar ta'bashi zaton ta idanunta ne ke hasko mata shi domin taganshi ne exactly yanda tayi mafarki dashi adaren jiya, bayyananniyar murmushi tayi aranta tacigaba da fa'din " da wannan daurarriyar fuskar tashi daba ko yaushe ake ganin sakewarta ba sai lokacin da yaga dama sannan kaga murmushinsa sai inko yana tare da Daddy ne wannan kam har zaka gaji da ganin dariyar tasa alokacin"
Daf da zata ta6a jikin madubin sai taji an ri'ko hannunta daga baya, hannun ta kalla inda aka ri'ke tan tabi hannun da kallo zaton ta ma Hannah ce sai kuma taga sa6anin hakan domin wannan hannun beyi kala koka'dan dana Hannah ba not even from her friends.
A 'dan tsorace ta kuma juyawa takalli cikin madubin sai taga wanda ke bayan tan ne yah ri'ke mata hannun nata, sai alokacin tunaninta yadawo dai-dai sai ta juyo afirgice zuwa inda yake tsaye 'din, gani tayi shi'dinne azahiri ba mafarki ba kamar yadda tasaba ba kuma atunani ba.
'Dayan hannun ta 'dago ta rufe bakinta dashi ta zaro idanu kamar wacce tayi karya tace
" _huh_! _Yayaah"!!!_ .Tafa'da ahankali bada bayyanan niyar sauti ba saboda bata manta irin tsawan daka mata ba ranar dayazo last kafin yau, shikuwa be amsa ba duk da yaji me tace saboda tun 'dazun tsayawa yayi yana kallonta sai ma 'kara binta da idanun dayake 'karayi yana wassafa abubuwa acikin ransa ciki harda irin kyan daya ga ta 'karayi, take sai yaji yana kishin duk wanda zai ganta a irin wannan yanayin.
Teemah data ga be yimata magana ba kuma be motsa daga tsayuwarshi dayayi ba har yanzun sai tayi tunanin ko irin mafarkan data saba yine, hakan yasa ta 'danji haushi harda turo baki gaba tana 'ko'karin 'kwace hannunta daga nashi sai shi kuma ya 'ki sakinta.
Teemah bata tsoron Yayanta na mafarki da tunaninta danshi be ta6a yi mata tsawa ba shiyasa bata wani jin shakkansa, ko yanzun ma dataga ya'ki sakin hannunta sai tace
" ka sake min hannuna yayah ni baruwana da kai, kullum idan naganka baka min magana sai de kayi shiru, inaso ma in baka ha'kuri tun ranar da kayi fushi katafi amma bansan yanda zanyi ba, saboda kullum kinmin magana kakeyi idan naganka"Rausayar da kai tayi gefe sai taci gaba da magana " kuma fah ba laifina bane dana 'ki gaya maka, ni bansan me zance bane alokacin koda nace zan fa'da 'din shiyasa ban 'kiraka ba".
Sake juyowa tayi ta kalle shi da sanyin murya tace " ka ha'kura yanzu yayaah?
Lumshe idanu kawai yayi ya kuma bu'desu akanta duk tana gani, sai de ita hakan be gamsheta ba sosai tagaji da irin hakan daya keyi ita so take ya bu'di baki yayi mata magana kamar yadda suka saba.
Data ga bashi da niyyan yin magana sai tace " sake min hannu na toh, Ummah fa'da zata min in tazo taga banyi wankan ba har yanzu "
Idanunta akan hannayen nasu tayi maganar.
" me yasa?
Haka kawai Abbas yace shima yana kallon hannayen nasu inda idanun Teemah yake." Baka gani ne?
yaufa za'a 'daura auren yah Mahmud wai....wai.... danii.
Ta'kara fa'da da jan maganar tare da sunkuyae da idanunta zuwa kasa.Duk da tana zaton wannan ma Yah Abbas 'din mafarkin ta ne amma haka kawai take jin nauyin sanar dashi maganar aurenta kai tsaye.
Tun ranar daya tafin nan kusan kullum sai tayi mafarkinsa ha kama tunaninsa yasako ta agaba kuma ko amafarkin ma ba magana yake mata ba, wani lokaci sai de tayi ta masa magana shi ya 'ki bu'dan baki yayi magana wani lokaci kuma sai tace tayi fushi itama sai tayi shiru suta kallon juna amafarkin.
Abbas da kansa ya gane cewa har nzu bata yadda shi 'din bane dakansa, domin yadda take yadda take yi masa magana ma ka'dai shaida ne.
Ga mamakinta sai taji ya mintsine ta ahannun daya ri'ke 'din hakan kuwa yasa ta ta 'dago da sauri ta kalleshi suka hada idanu, rintse idanun tayi da 'karfi ta kuma bu'dewa a 'ko'karinta naganin ta tashi daga baccin da takeyi 'din, amma ko da ta bu'de 'din ma sai ta sake cin karo da fuskarsa agabanta still yana kallonta, baki ta bu'de da niyar yin magana sai ya ja hannun nata da sauri ya janyo ta zuwa jikinsa, ha'da bayanta da jikinsa yayi sai ya juya ga dressing mirror 'din, sai ya zamana dukkansu suna fuskantar madubin, kwantar da kansa yayi agefen kafa'darta yace
_"_ _oyah tell me now"!_
Shiru tayi bata yi masa magana ba illah kallonsa data cigaba da yi sai shine yasake fa'din _" bani ha'kurin yanzu inaji"!__Comment_ 🖊
_Vote_ *⃣ and
_Share_ 🤞🏻 pls_My fellow_ _wattpadians jinjinar_ _bangirma Allah ya bar 'kauna.........I heart u all._
*Salmern ku ce*😍
YOU ARE READING
CAPTAIN ABBAS
General FictionMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...