P72

1.7K 99 7
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

~Dedicated 2 my family~

*Bismillahir rahmanir raheem*


_*3 C’s of LIFE* : Choice, Chance & Change – You must make a choice to take a chance or your life will never change._

🅿 *72*

'Bangaren Hannah kuwa harta gama shirinta tafito bata ga Hannah ba sai ta yi gurin Ummah dan ganin ko tana can ne, amma kuma sai ta tarar da Ummah zaune  ita ka'dai, tambayar Ummahn tayi tace " _Ummah ina Teemah fa ko de tagaji da jirana ta wuce abinta dan naga_ _yau zumu'di_ _takeji_ _dashi_ "

Murmushi Ummah tayi tace
kafin ma ta rufe bakinta sai Ummah tace mata " _Ta kaiwa Yayanku abin sha ne bari ta dawo_ "

" _Yayah ya zo ne dama Ummah_ ?
Hannah ta tambaya lokacin tana shirin zama agefen Ummah.

Amsa ta bata da fa'din " _ehh be ma da'de da isowa ba yanzun nan ya shiga ciki, kije mana ku gaisa_ ".

'Dan 'karamin tsaki Hannah tayi tace " _barshi Ummah sai mun dawo kawai naje kafin nan ma kinga ai ya 'dan huta_ "

'Dan hira suka 'dan fara ta6awa da Ummahn kafin Teemah tazo, anan ne Ummah ke sanar da Hannah batun zuwan Mummy harma da Anty da Teemah tafa'da mata.

Hannah tayi murna sosai har zuciyarta da jin cewa Mummy zata zo saboda ita kam tana son Mummy ko dan goya mata baya ma datake yi akan komai sa6anin na Anty data kya6e baki tace " _Allah ya kwaota lafiya_ "

Teemah kuwa nacan tana aiki tana share hawaye, haushi gaba 'daya ya bi yacikata shima Abbas yana tsaye har yanzu be motsa ba har ta shiga tagama kintsa bedroom 'din ta wanke bathroom ta fito yana nan tsaye ,tasan cewa zefi fara bu'katan can 'din kafin parlour shiyasa tafara gyara cikin.
Tana aikin takaici fal zuciyanta tarasa meke damunsa shi akullum yafi son yaga ya 'kuntatawa mutun in bahaka mi ye ruwansa da fitan su harda zai ce wani bazasu fita yau ba sai gobe, salon yanuna halinsa afili kawai, bayan gobe Mummy da Anty zasu zo shine kuma zata fita yawo? tama rasa me ya dawo dashi wallahi, mutum sai fitinan tsiya.

Yana nan tsaye, yana tunanin yanda yaga yau duk ta canja tayi wani kyau na musamman da ita, duk da yake dama ita 'din me kyau ce amma na yau 'din na musamman ne, sai de har yanzu tana nan arame bata mai da jikinta nabaya ba.

Hawayen da yaga take ta sharewa ne ya 'dan 'dauki hankalin sa sai ya fara bin duk wani moves 'dinta da idanu, gani yayi da gaske kuka takeyi da hawaye, alokacin ma barta kammala shara ta goge ko'ina saura goge center table 'din dake tsakiyan parlourn ne ka'dai yarage take kan yi, sai ya taka ahankali ya isa inda take.

Hannunta ya kama ya mi'kar da ita tsaye sai kuma ya tsaya yana 'karewa cikin idanun nata kallo, 'kasa tayi da nata idanun jin gaba 'daya sun mata rauni, sam yanzu bata iya juran kallon tsakiyar idanunsa, intayi hakan kuwa jikinta har rawa yake 'dauka gaba 'daya, Yayah Abbas kwarjini yake yi mata sosai.

Ko yanzun ma 'kasa tayi da nata idanun hawayenta na sake gangarowa ahankali.

Da yatsan sa 'daya  ya shafo hawayen nata sai ya sake nuna mata a saitin idanun ta wanda dolenta ta 'dago ta kalli yatsan daga nan ta 'dan kalle shi ka'dan, suna ha'da idanu sai shi ya sake bu'de nashi tare da 'dage gira sama da sauri tayi 'kasa da kanta ahankali yace " _dan nasaki aiki kike yin kuka_ ?

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now