P65

1.4K 84 1
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

Dedicated 2my lovely fans da ke ~whattsapp~
~facebook~ &
~Wattpad~
Inayinku sosai nima,
Allahu ya bar 'kauna.

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir rahmanir raheem*

_True friends are not the ones who are there when it’s convenient. True friends are there when it’s not._

🅿 *65*

Sa'kon gaggawa ne ya iso musu cewar kayan da za'a kawo musu a Lagos za'a sau'ke su so sai aka wakilta Abbas akan zuwa kar6o kayan, dama da farko  maiduguri za'a taho da kayan direct sai kuma aka samu wani matsala inda dole sai de a sau'ke a Lagos sai suje su 'dauko.

Ko ka'dan Abbas be kwana da niyyan tafiya ba amma da asubar fari aka sanar dashi lokacin ma yana zaune dafe da kansa bayan farkawar da yayi daga bacci da mafarkin Fateemah sosai mafarkin ya tsaya masa aransa, wai tana ta kuka saboda tarasa hanyar zuwa ko'ina ne oho, duk inda tabi de sai taga gurin yah mata duhu gashi wai tana ganinsu agabanta sun kewaye ta, a wurin akwai Mahmud, yaga Hannah, Antyn Mahmud yaga Daddy ma da kuma wasu mutane kimanin biyar da be sansu ba, amma inda akwai hanyan 6angaren Mahmud ne, Antyn Mahmud, wata da be santa ba da kuma shi kanshi, so take ta wuce amma tarasa ta ina zatabi, cikin wa'yancan ukun duk inta bi 6angarensu duhu ke mamaye gabanta, dalilin haka sai ta sake sakin kuka tana yarfe hannu, shi ka'dai ne kawai 6angarensa be yi mata duhu ba, amma ko data biyoshi 'din sai hanyan yayi mata nisa sosai yanda zai yi mata wahalar cimmasa shi kansa ma nisan yayi mata tana hangoshi yayinda har hannunsa yake mi'ka mata dan ta kama amma bata iya kamawa, hakan sai yasa taci gaba da kuka tana fa'din " _Yah Abbas_ !
_Ya...... Abbas_ !!
Yana san taimaka mata shima amma sai ya kasa, Mahmud kuwa daganin tana bin inda Abbas 'din yake tana 'kiran sunan shi sai shi kuma ya juya bayansa yana murmushi, taku 'daya biyu zuwa uku yayi sai ya 6ace 6at suka daina hangoshi sai haske ya mamaye gurin gaba 'daya tare da wani lumshi me 'kayatarwa.

Dai dai 6acewar Mahmud 'dinne Abbas ya farka daga baccin yatashi ya zauna dafe da kansa yana sake bitan mafarkin dayayin tare da juya al'amarin acikin ransa, yarasa ma'anar mafarkin gaba 'daya, abu 'daya ya iya fahimta shine Fateemah na bu'katar taimako arayuwarta sai de be san dalilin da ze kawo hakan ba.

Yana cikin tunanin mafarkin ne sai ya samu sa'kon tafiya zuwa Lagos, wanda  yazo masa a bazata a kuma dai dai lokacin da ze fi bu'katan hakan, haka ya tashi yayi komai cikin hanzari ya gama shirinsa tsaf.

Su shida suka tafi , jirgin 'karfe 6:30am na safiyar ranar juma'ah suka bar Maiduguri zuwa Lagos.

Sai dai kuma cikin rashin sa'a sai da suka isa Lagos suka sake tarar da sa'kon cewa sai zuwa yamma zasu iso dan haka sai suka nemi gurin da zasu huta kafin yamma amma sam basuji da'din hakan ba.

Da wannan damar Abbas yayi amfani ya nufi office 'din Mahmud wanda a'kage yake yaji ya Fateemah take agurin Mahmud 'din, dan shi gani yake kamar rashin son auren da Mahmud yace baya yi ne yasa shi ya kasa kula da ita, be san gidansa ba office 'dinsa yasani dan haka sai ya nufo office 'din,  yana da tabbacin adai dai wannan lokacin Mahmud na office.

*****
Fateemah da Mahmud kuwa basu suka isa office 'din ba sai 9:13am
dayake ansamu ha'duwar holdup sosai ahanyar shiyasa ma suka 'dan 6ata lokaci kafin su isa.

CAPTAIN ABBASМесто, где живут истории. Откройте их для себя