💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*_Dedicated to my family_ .🥰
*Bismillahir rahmanir raheem*
_The greatest thing in life is finding someone who knows all ur mistakes nd weaknesses nd still loves u nd thinks u ar d best thing in there life!_🅿 *87*
A haka Hannah ta fito daga bathroom 'din ta same ta tana murmushi ita ka'dai.
Batayi mamaki ba dan hakan sai tace " luv thing-thing"
"Ke kika sani ai amoebo"
Dariya Hannah tayi tace "na canka dai-dai kenan?
Teemah batayi magana ba sai tayi murmushi kawai ta sake d'ago wayar ta.
" _murmushin fa na menene ko duk na soyayyar Yayah ne_ ? Hannah ta tambayeta.Teemah sai tace
" _ke ni 'kyaleni Mummy zan 'kira_ "" _Zama ki fa'di gaskiya ai_ "
Hannah tace tana mai goge jikinta.Teemah Mummy ta 'kira da Anty duk suka gaisa da yake tana cikin farin ciki tayi 'kiran shiyasa ta sanya zu'katan su suma cikin farin cikin sosai ganin ta saki jiki agidan ta.
Da Mummy ta tambaye ta lafiyar ta sai tace " _lafiyata 'kalau Mummy, amma yanzu kullun bana iya bacci mai kyau da dare kuma sai in tajin yunwa sosai kuma fah bana son hakan ni Mummy_ "
Murmushi Mummy tayi dan tashin farko ta fahimci meke damun Teemahn amma ganin bata sani ba itan sai Mummy ma ta bita a hakan tace da ita "bakomai ai is normal watarana bazatayi hakan ba"
Kafin tayi maganar Hannah tazo ta 'kwace wayar ta kai kunnan sannan tace da Mummy " _Allah Mummy Teemah chop-chop ta zama sai kinga yanda tazama, har ta nin kani sau biyu_ "
Hannah kam harda kari tayi dan bawani jikin kirki har na azo agani Teemah tayi ba kawai dai ta d'an canza ne kuma bai 6ata ba sai kyau da wani fresh ta sake yi abinta.Teemah na daga inda take tace " _Allah Mummy 'karyan Hannah ne dama ita ai tsililiyace kawai tana kishi dan taga na fita kyau ne_ "
" _Hmmm, Toh Allah dai yasa lafiya ne_ "
Fa'din Mummy kenan tana murmushi.Da haka suka gama wayar kowa na farin ciki haka kawai suka tsinci kawunansu cikin annashuwa da farin ciki mara misaltuwa.
Bayan sun gama da wayar ne Hannah ta bawa Teemah labarin zuwan Bilal, akan yace zai dawo ayi maganar auren su sai ya koma.
Teemah najin haka tace " _kice nima dai na kusa in huta da rainon ki kenan_ "
Hannah da wuri ta tare ta da fa'din " _kut amma kin gama dani wallah, ni dake waye me rainon wani fisabillahi, duk_ _wahalan da kike bani ki hana ni baccin dare ki hanani sakewa a gado shine zaki ce wani kina raino na, ni Allah ma yasa_ _Yayah ya tafi dake can garin na huta da rigimar ki_ _wallahi_ "
Musu suka hau yi a tsakanin su kowa na depending kansa kamar wasu 'kananun yara har sai da Ummah tazo sannan sukayi shiru.
Hannah da Teemah ne sukayi girki da dare, Ummah tayi-tayi su bari ko dan saboda Teemah ma amma suka 'ki, bayan sun gama suka sake yin wanka sukayi sallar maghrib da isha'i sannan suka ci abinci.

ESTÁS LEYENDO
CAPTAIN ABBAS
Ficción GeneralMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...