P64

1.5K 84 3
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*


*Bismillahir rahmanir raheem*

_Laugh when you can, apologize when you should and let go of what you can’t change........_

🅿 *64*

"Fateemah kigaya min meyasa baki son zama agidannan idan ke ka'dai ce?

Da rawar murya tabashi amsa da fa'din" banace maka tsoro nakeji ba"

" Tsoron me kike ji inason yau ki gaya min"
Mahmud ya fa'da da sauri.

Kame kame tafara tarasa ma me zata ce dashi
sai ni.......ni....tsoron.......
ts

Ganin batada niyyan fa'da masa sai yasake jefa mata tambayar su waye suke zuwa gidan nan idan baya nan.

Da sauri tace
"Bakowa "
Tana rarraba idanu.

Shima ce mata yayi " 'karya kikeyi  Fateema nasan akwai, ki fa'da min zansa ayi maganinsu kinji, bazan ta6a bari su cutar min dake ba muddin ina numfashi, ko kinfiso kullum ki dinga zama agidan mutane yafi miki akan gidan mijinki?

Shiru tayi tana sauraransa sai ya kamo hannayenta yari'ke acikin nasa da sigar lallashi  yace
" _Fateema nifa mijinki ne,me burin ganin farin ciki da walwalarki akowani lokaci, meyasa kika_ _za6i ki 6oyemin damuwarki bayan ni yakamata in fara sanin me_ _kike ciki amma sai de naje naji awani guri Fateema kinajin hakan kinmin adalci_ _kenan_ ?
_nine fah me hakkin kula da duk wani hakkinki da_ _damuwarki ayanzun meyasa bazaki bani wannan matsayin ba_ "

Fateemah kam haushin kanta take ji ayanzun dan tasan da bata nemi jin damuwarsa ba da baze tuhumeta da wannan maganar a dai-dai wannan lokacin har haka ba, ita kuwa ayanzun da jiran zuwan Daddy kawai takeyi me zesa tafa'da masa abinda ke faruwa, kalan aje akasheta kafin Daddy yazo.

Shirun da Mahmud yaga tayi masa ne yasa shi bu'dan baki yana 'karfafa mata zuciya da fa'din
" _kar kiji tsoro Fateemah karkiyi kokwanto ko shakka dan Allah ki gaya min kinji_ _am always here 4u_ "

Kalmar nan dayafi tsana tasake maimaita, masa wato " _bakomai fah Yayah in akwai ai zan gaya maka_ ....

Kallonta yayi cikin idanu domin zuwa yanzun haushi tafara bashi
" _Fateemah kina ganin kamar 6oye min damuwarki shine zai kawo miki masalaha acikin_ _al'amuranki ko_ ?
_Shikenan idan hakan kike ganin yafimiki so be it nima bazan damu_ _ba, bazan 'kara damuwa da irin hakan ba tunda baki san ina shiga_ _lamuranki_ !"

'Kasa tayi da idanunta da suka cicciko da hawaye tsawon mintina biyu bata 'dago tasake kallonshi ba, hakan yasa Mahmud ya fahimci cewa bazata sanar da shi 'din ba kenan.

Tashi yayi da sauri ya tsaya tare da sa hannunsa 'daya ya naushi cikin 'dayan da 'karfi.

Kansa yadafe zuciyarsa na masa suya sam yarasa ya zaiyi da ita, 4d first time arayuwarsa da taurin kan Fateemah ya 6ata ransa, daya san bazata sanar dashi ba da be bari Umar yatafi batare da ya sanar dashi ko suwaye suke neman lalata masa rayuwar mata ba.

Damuwarsa be wuce yasan kosuye ba, domin yana mamaki, tsawon watanni biyu kenan da zuwan Fateema garin Lagos amma be ta6a jin tamasa hiran wasu da tasani anan 'din ba, kamar yadda yasan bata ta6a fita da sunan ziyartar wani gida ba haka itama bayaga Anty mahaifiyarsa babu wanda ya ta6a zuwa gidan nasu hatta abokansa tun bayan aurensa basu 'kara zuwa ba, mamakinsa shine ya akayi masu neman nata suka santa, da wani lokaci kuma a ina da har zasu nemi maida masa ita jinsin 'yan ma'digo.

CAPTAIN ABBASKde žijí příběhy. Začni objevovat