💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*~Dedicated to my fans.~
*Bismillahir rahmanir raheem*
_If you treat her the same way you treat others, how is she supposed to know that she is special to you....?_
🅿 *75*
Ranar da Hannah taji labarin cewa Teemah ne Yayah Abbas zai aura ba 'karamin farin ciki tayi ba, sai de kuma tana jin tausayin Teemah ka'dan saboda halinsa, amma damuwar ta be yi yawa ba danta fahimci cewa tsakanin Teemah da Yayahn akwai wani 6oyayyen sirri da har yau takasa gane ko menene shi.
*****
Sai da bikin ya rage saura kwana biyu kafin Daddy yazo, hakan ma Mummy ce ta matsa masa akan yayi saurin zuwa saboda Teemah, amma da shi niyyan sa sai ranan Thursday zai taho inyaso friday sai a'daura aure aranar kuma sai ya wuce lagos saboda auren Abbahn Mahmud da za'a 'daura ranar saturday.Amma da Mummy ta matsa kawai sai ya taho, ganin sa kuwa har sai da ya sanya Teemah kuka taje da gudu tafa'da jikinsa tana ta rungume shi tana kuka, Daddy kam murmushi yayi ya dinga bubbuga bayanta ahankali yana bata ha'kuri harta yi shiru sannan sukayi gaisuwa me kyau da ita ha kama Hannah da suka zo gaida Daddyn tare.
Hannah kam mamaki ba 'karamin cika ta yayi ba na ganin shagwa6ar da Teemah ke yiwa Daddy dan ko ita da take auta ma wani abin idan Teemah tayi sai dai ta tsaya kalonta dan ita bayi take ba duk kuwa da take autar gida ce ita, kuma Yayah Abbas ne ya hanata, dan baya barinta aduk lokacin daya ga tana yiwa Ummah shagwa6a taka mata birki yake yi 'karfi dayaji sai da ya hanata.
Tun shigowan su ta kama guri ta zauna tayi shiru tana jiran Teemah ta gama kukan dan gani da tayi hankalin Daddy gaba 'daya ya koma kanta da rarrashin ta kamar wata yarinya 'karama.
Dasuka gaida shi kuwa suka fito ahanyar koma wan su Hannah ke tsokanan Teemah cewa " _taji kunya ai da shagwa6a kamar wanda Daddyn goya ta zai nayi dan ta da'de bata ganshi ba shine harda irin wannan kukan?_ "
Tayi maganar tana ta6e baki.Amsa Teemah ta bata da fa'din
" _Anyi 'din ina ruwanki_ "Kai Hannah ta ka'da taci gaba da tafiya take fa'din " _hmm, kiyi dai a hankali dan ina jiyake miki watarana, wannan_ _irin shagwa6an sai kace wata 'yar shekar uku? ke da_ _aure ke gabanki_ "
Azafafe Teemah tace
" _ai kema auren ne ke a gabanki tunda kema macece_ "" _Nasani ai shiyasa ma nake gaya miki, shi aure ai duk sunansa aure, amma kuma mazan kala-kala_ _ne_ !"
fa'din HannahTeemah kuwa cewa tayi
" _shiyasa ai naga kina wa Bilal shagwa6an kuma yana kar6a miki tun_ _ma kafin yazama mijin naki_ "Dariya Hannah ta saka sannan ta juyo ta kalli Teemah tace tace " _aini nawa daban ne dan indai Bilal ne ze kar6a min fiye da haka ma shiyasa ma ai nace miki mazan_ _kala-kala ne_ "
Tafiya Teemah ta fara tare da fa'din " _nima indai mijin irin Yah Mahmud ne toh bana fargaba koka'dan_ "
Da gudu Hannah tasha gabanta tace
" _Waye ya gaya miki irin marigayin mijinki ne_ ?
_naki tamkar dodo yake inkin ce zakiyi ta masa haka wahala zaki sha_ "
YOU ARE READING
CAPTAIN ABBAS
General FictionMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...