P37

1.2K 79 0
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍


*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi masoyana*


*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

"Time is free, but it's priceless.
You can't own it, but you can use it.
You can't keep it, but you can spend it.
and once you've lost it you can never get it back."

🅿 *37*

Koda ta idar bata bi takan kwalin ba har yanzu, kwanciyarta kawai tayi sai dai tana kwantawan mummy ta fa'do mata arai kawai sai ta mi'ke da hanzari tatafi wurin mummyn dan tasan dole zata damu idan tajita shiru.

Murmushin 'karfin hali ta 'ka'kalawa fuskarta yayinda ta tunkari inda mummyn take, koda mummy taganta ahakan kuwa sai ta 'dan ji dama dama.

Murmushin tayi itama sannan tace
" yanzu kuwa nake so na aika aduba minke sai kuma gashi kin fito"!

Batayi magana ba sai da ta 'karasa kusa da mummyn ta zauna kafin tace " kaina ciwo mummy sosai"
tayi maganar tana wani yatsine fuska tare da dafa goshinta da hannunta 'daya.

" haya niya ai, bari anemo miki magani kisha zaki d'anji daidai".

Mummy tayi maganar tata cikin kulawa sai ta 'kara da fad'in " ki koma 'daki ki kwanta ki 'dan huta idan ankawo maganin sai kisha ".

Kai Teemah ta 'daga alamar " toh tare da mi'kewa tsaye ta kama hanyar 'dakin nata.

Koda takoma 'dakin kuwa kwanciya tasakeyi, so take tayi bacci amma sam sai taji takasa yin baccin ma fuskar Yayanta ka'dai ke yimata gizo tana ganin tamkar bashi 'din bane dagaske tagani.

Wayarta da tun safe take ajiye a gefen mirror itace tayi 'kara alaman shigowan sa'ko kuma 'karan ne ya yanke mata tunanin yayantan datakeyi.

Kuma sai alokacin ma ta tuna da wayarta saboda tunda tafara shiri bata 'kara bi takan wayar ba sai da tagama shiryawa ne ta 'dauko wayar ahannunta ta kashe selfii bayan tafito da nufin tafiya wurin graduation d'in sai kuma ta ji ri'kon wayar ya dameta shine ta aiko aka ajiye mata ad'aki.

Toh shiyasa bata 'kara bi takai ba sai kuma yanzun dataji wayar tayi 'kara.

Ahankali ta tashi taje ga wayar bawai dan 'karar sa'kon dataji ba " a'a " kawai jii tayi tana bu'katan ganin cikin wayar tata da ta 'dau tsawon awanni batare da sun gana ba.

Dawowa tayi ta kwanta rigingine kanta nakan pillow yayin da 'kafafun ta ke ajiye akan katifa ta wani had'esu guri d'aya.

Koda ta bu'de wayar sa'kon Mahmud tafara cin karo dashi a fuskan wayar ga dukkan alamu shine sa'kon da ya shigo 'karshe 'dan mintina 'kalilan dasuka gabata .

Bud'e sa'kon tayi domin ganin me aka rubuta mata .

" wai nayi laifi ne bansani ba? "
Haka taga anrubuta

Sai tayi reply da " haba laifin me zakayi kuma yayah"!

Daga nan tabar wurin messages 'din ta koma taga tarin missed calls 'din data tara duk daga yayanta Mahmud.


CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now