💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*Dedicated to all Naija's PEOPLE.
*HAPPY INDEPENDENCE NIGERIA* (59th anniversary)🇳🇬. My nation my proud....Nigeria d promise land, the great nation..👍*Bismillahir rahmanir raheem*
_Time passes, memories fade, feelings change, people leave but hearts never forget_ .🅿 *88*
Bayan sallar azahar yace da ita ta shirya su fita yawo, Teemah kam take tafara murna da farin ciki ta wuce 'dakin ta, cikin 'kan'kanin lokaci tayi shirin ta cikin wata Arab gown baki mai 'dan fa'di musamman daga 'kasa dan daga saman ya dan kamata, sosai rigar ta kar6i jikin ta.
Light make-up kawai tayi inda ta shafa powder kawai sai ta sanya wa idanun ta kwalli sannan ta shafa lipstick ja.
Veil 'in ta ta 'dauko tayi rolling da shi ta sanya flat shoe a 'kafar ta tare da 'daukan wani 'dan 'karamin side bag mai kyau da tsada, har zata fita sai kuma ta koma ta 'dan fesa perfumes kala biyu sama-sama kasancewar ta mai masifar son 'kamshi.
Cikin natsuwa ta isa 'dakin sa ta tura tare da yin sallama ahankali.
Abbas ma a hankalin ya amsa tare da yi mata kallo 'daya sannan ya juya yaci gaba da abinda yake yi.
Teemah kam baki ta ta6e aranta tace " _mutun kullum sai fama da longslip shirt kamar abin ibada_ "
Bakin gado ta isa da niyyan zama amma kafin ta zauna sai taji yace da ita " _zo nan Zahra"_
Fasa zaman tayi sai ta cire jakar tan ta ajiye abakin gadon sannan ta 'karasa inda yake tsayen, tana 'karasa wa ya juyo gareta tare da 'dauke hannun sa daga kan 'kirjin nasa yace " _help me plz"_
Bata sha wahala wurin gane abinda yake nufi ba ganin gaban rigar sa abu'de, abin mamaki ma duk kokuwar dayake ta faman yi 'din guda biyu kawai ya sanya.
Badan farin singlet 'din dake jikinsa ba da dukkan 'kirjinsa afili zata gani dayake daga 'kasa yafara 6allewa sai itama takama daga wurin tacigaba har zuwa sama.
Yana son amfani da irin kayan amma har yanzu yakasa sabawa da 6alla bottles 'din riga cikin sauri.
Abbas kam shiru yayi yana bin fuskar ta tare da sha'kan dad'd'an 'kamshin da jikin ta ke fitarwa.
Within a minute Teemah har ta gama 6alle masa bottles 'din tana 'ko'karin sau'ke hannun ta daga 'kirjinsa kawai sai ya ri'ko hannun yana kallan cikin idanun ta da murmushi yace " _kinyi kyau fa amma ka'dan_ "
Murmushin tayi itama dan tasan tsokanan ta kawai yake yayi kuwa bata son 6ata lokaci yanzun ta 'kagu tagan ta a mall shine babban burin ta ayanzun shiyasa bata ja maganar ba.
Dan haka itama sai tace dashi " _amma ai na fika kyau duk da haka tunda nayi make-up kuma kaga kai bakayi ba_ "
" _Really_ "
Ya fa'di tare da 'dage gira sama yana murmushi yace " _let see_ "
Tare da matso da kansa kusa da nata tana 'ko'karin jan baya sai yayi saurin 'dora bakin sa saman nata yafara bata wani passionate kiss mai shiga jiki.Teemah tun tana 'ko'karin 'kwace kanta har ta zo ta ha'kura kasancewar gwiwoyin ta da suka yi mata nauyi, daga 'karshe kuma sai tafara jin zafi sosai abakin nata, hawaye tafara sau'kar wa sirara na azaba wanda ganin hakan yasa Abbas sakin mata bakin sai ta koma ta rungume shi tana mai ci gaba da tsiyayar da hawayen a hankali.
YOU ARE READING
CAPTAIN ABBAS
General FictionMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...