💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍_Wattpad@_
_Serlmerh-md_💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫~We are here to~ ~make you~ ~happy,smile,educate~ ~and to~ ~realized~ ~that we are the best~ ~among all~ .....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO**Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
🅿 *4*
Shirye-shirye aka farayi na tafiyar abbas 'din makaranta,dayake hankali bai gama isan Teemah ba shiyasa bata wani damu da batun tafiyar ba har se ranar da ze tafin kafinnan, wato ranar laraba.
Dawuri yagama shirinsa don shima irin yaran nanne masu jarabar son makaranta.Baya wasa da harkar karatun shi tun asali,wannan halayyarsa ne tun yana yaro qarami.
Ballantana Yanzu da ya 'kara wayo sai ya fi jin yin karatun sosai.11:00am ne flight dinsu,ba sassafe zasu tafi ba,hakan yasa yau 'din ma yace shi ne zai kaita makaranta.
Ahanya neh yake sanar da ita cewa shima fah zai tafi makarantarsu anjima,ko ajikinta bata damu ba illah cewa datayi "ai nima zan dinga raka ka kullum inzaka je"
Dariya ma tabashi shikam,dan shirman nata abin dariyah ne, wannan shi ne ana ce miki ga gabas kina 'kara tambayar ina al'kibla.
Sai da yayi dariyar kuwa sannan yace mata
" ke bafa anan bane makarantar,tafiyata zanyi nima,yanzu sai de Habibu ya rin'ka kawoki a mota kullum."
Kanta ta lan'kwasa gefe 'dayan kafa'darta tare da fadin
"hum um-hum um"
harda bubbuga kafafunta a'kasa irin na shagwa6a66un yaran,sannan tace ni banaso.
Kallonta yayi sosai dan so yake ta fahimci maganar tasa sosai amma yarinta bazai barta ba sai kawai yace mata"dolenki ai yarinya,inkuma bahaka ba sai de ki rin'ka zuwa ke ka'dai."Kinga habibu ma huta da zirga- zirga.
Kuka tafara masa na rashin dalili,ehh mana rashin dalili,daga cewa habibu ne zaina kawota makaranta kuma sai kuka,toh danma bataga yatafi yabarta ba kenan daya zatayi. abin dariyah wai
cewa tayi .
"sai na fa'da ka da Daddy"Batasan cewa daddyn shi ne jagoran tafiyan ba.kiyi ha'kuri karki fada ni da daddy ya fa'da da sigar yanda itama tayi magananta,ta ke kuwa yabata dariyah."me zan siyo miki idan naje makarantar ya tambayeta."ai nima binka zanyi inzaka tafin,irin yanda kake rakani,a'a nawa nikai zanje bawanda zai rakani kuma idan natafi zandade bandaqo ba.amma wannan karon bata kulashi ba don yafara bata haushi.sai kuma ta tuna fruits 'dinta
Kai ta 'daga ta kalleshi,hannunta na ri'ke cikin hannunsa suna tafiyar.sai tace toh yayah idan katafi wazai dinga siyamin Apple da pineapple harda babana ma?
Habibu zaina siyamiki kinji? Yabata amsar tambayarta ta cikin sauri. Kuka tafara masa wai ita bata son na habibun nashi take so.suna tafiyah tana kuka,tausayinta yakeji dan yasan dolene daman taji ba da'di,shikansa ma bada'din yakeji ba don sosai sukayi sabo fiye da zaton mai karatu.
Da 'kyar ya lalla6eta tayi shiru sai da yace mata dawasa yake mata babu inda zaije.Kuma shine zai na siyamata apple 'dinta kullum.
tana jin haka kiwa kuka ya 'dauke cak.
Haka ya rakata makarantar dai dai zata shiga ya miqa mata lunchingbox 'dinta yace ta shiga class dinsu banda wasa,harta fara tafiyah sai ya 'dan 'daga 'kafa ka'dan ya iso gareta,dayake bata wani yi nisa da inda yake tsayen ba,hannunta yakamo sannan ya tsuguna dai dai tsayinta.Sake daidaita mata 'dan Hijab 'din uniform 'din dake kanta yayi,wanda dudu-dudu bai wuce iyah kafa'dunta ba.
Kallon cikin idonsa tasa keyi itama,sai yayi murmushi ya kamo kumatunta duka biyu ya 'dan jijjiga mata fuskar
ESTÁS LEYENDO
CAPTAIN ABBAS
Ficción GeneralMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...