P52

1.3K 76 1
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs _ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

 
_People_ *change* , _love *hurts* , friends *leave* , things *go wrong* but just remember that life still_ *goes* *on* .

🅿 *52*

..............,Abbas lumshe idanu yayi jiyayi da 'ace shi ka'dai ne awurin da babu abinda zai hana hawayen shi zuba a dai-dai wannan lokacin amma yanzu kam daya kasance acikin mutane, mutanen da bazai ta6a iya sanin yawan su ba sai kawai yace _" Allah_ _kaine gatana, Allah_ _ka ji6anci_ _lamura na"_.

'Daurin auren ba 'karamin al'ummar annabi ya tara ba kama daga kan manyan 'yan kasuwa da manyan 'kusoshin gwamnati da sauran jama'ar musulmai baki 'daya.

Mahmud da kansa sai da yaji fa'duwar gaba, zuciyarsa tsinkewa tayi da 'karfin gaske  _innalillahi wa innah_ _ilaihirraji'un_ dukkansu suke faman ambata azu'katan su.

Abbas ne ya daure ya 'ka'kalo murmushi na dole ya azawa fuskarsa  sannan ya ciri hannunsa ya mi'ka wa Mahmud suka yi musabiha " _Inai muku fatan Alkhairi 'dan uwa, Allah ubangiji ya baka ikon yin ri'ko da gaskiya da amana ya sanya fahimtar juna a tsakaninku"_

Shima Mahmud murmushin ya 'ka'kalo yayi wanda ta tsaya masa a iya saman la66ansa ko ka'dan ba wannan bane azuciyarsa amma dan kawai ya nuna wa Abbas 'din yabawa da  godiyarsa sai ya 'kir'kiri murshima shima sai yace " _Ameen-Ameen Yayan mu godiya marar iyaka"._

Kasa sake hannun Abbas 'din yayi suka tsaya ahakan, Abbas gefe ya maida idanunsa yana jinjina al'amarin ubangiji acikin ransa, in just a month gashi an raba shi da farin cikinsa, wannan aikin kam sai de a'kira da _'kaddara_ saboda shi koda wasa be ta6a tunanin faruwar hakan ba yariga ya barwa zuciyarsa cewa Teemah tashi ce shi yasa be ta6a damuwa ya kauda irin hakan ba, sai gashi rana tsaka ta inda bai ta6a zata ba, aka datse masa mafarkinsa batare da kai ga idda shi ba, sai gashi Teemah ta barshi,  bari kuma na har abada.

  Tunda suka gama maganganun su kowa sai murmushinsa ya kau.

Abbas na so ya cire hannunsa daga cikin na Mahmud amma sai Mahmud ya sakin masa hannun, dole tasa ya dawo da kallonsa ga Mahmud 'din gaba 'daya.

Idanun Mahmud na cikin na Abbas 'din yace _" Abbas_ _nagode, nagode_ _sosai da irin 'kokarin 'da kai ta faman yi akaina dan ganin na cika BURIN mahaifina_ ,  _nasani cewa mai sonka shine wanda  akullum yake 'ko'karin ganin baka_ _kauce hanya_ _ba, wannan itake tabbatar da son gaskiya da aminci!, Abbas yau gashi BURIN_ _ABBAH NA yacika, amma ni na kasa jin farin ciki azuciyata, inajin tamkar bazan iya ba, inajin tamkar_ _wani gagarumin nawi ne ya hau kaina, Abbas taya kake ganin zan_ _iya ri'ke wannan babbar amanar bayan ban shirya amsar ta ba?"_

Abbas 'din sai yace mishi
_" Daure wa zakayi Mahmud, nasani cewa nauyi ne, nauyi ne ya hau kanka Mahmud sai de ba irin wanda kai kake zato ba, kai dai kawai ka mi'kawa Allah komai nasan zai maka jagora"_

Ahankali ya janye hannunsa daga cikin na Mahmud da ya tsaya shiru kamar me tunani dafa kafa'darsa Abbas yayi sai ya 'dago ya kalli Abbas 'din Abbas sai ya daga girarsa sama batare da yayi magana ba, ya kuma 'dan juya jajayen idanunsa yayi wa Mahmud nuni ga mutanen dake gurin.

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now