💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
Don’t confuse your path with your destination. Just because it’s stormy now doesn’t mean that you are not headed for sunshine.
🅿 *45*
Daddyn Abuja ne ya sanar da Abbas 'din cewa da safiyar yau suma suka wuche Jihar Yobe, sosai Abbas yaji haushin rashin samun sun da be yi ba, har ma yace wa Daddyn nasa " me yasa toh suka tafitun yau"?
Cikin jin haushi yayi maganar." haba Abbas ka manta bikin waye za'ayi ne"?
daddyn ya tambayeshi da mamaki.Kauda kansa yayi gefe sannan yace " ban manta ba Daddy kawai naga sunyi saurin zuwa ne ai dasun bari ranar Wednesday ko Thursday sai su tafi".
"Yanzu kam ai shikenan tunda sun tafi komai ya wuce, in ganin su kake son yi ka bi su can 'din."
Shiru yayiwa daddyn nasa bai tanka ba,kawai ya tashi ya nufi 6angarensa domin watsawa jikinsa ruwa.
Daga lokacin da ya iso zuwa daren ranar tsakin da yayi yafi sau a'kirga, abubuwane suka taru suka mar yawa acunkushe ya ringa jin zuciyarsa , koda yaji yunwa ta dameshi sai ya nemi abinci anan ma Daddyn Abuja yace yajira akawo abincin ya aika asiyo.
Ka'dan yarage tsakin da yayi azuciyarsa tafito fili Allah ya taimakeshi azuci yayi ta shiyasa Daddyn nasa be ji ba.
Sai kawai ya tashi ya nufi harabar gida amma sam yarasa inda zai samu nutsuwa, tunani yayi ko de ya shiga cikin gari yawone?,
Toh inka fitan ma ina zaka nufa?
Wani 6angare daga zuciyarsa ta tambayeshi.Safa da marwa ya fara yi agurin yana tunani " wai dagaske ne za'ayi auren kenan?,
Dagaske Mahmud ne zai auri Fatima bani ba"." ehh dagaske ne mana tunda gashi su Ummah ma sun tafi domin halartar 'daurin auren".
Wani 6arin zuciyarsa ne ya sake bashi amsa.
Tambayar kansa da kansa yayi wai " me yasa duk wani abu daya shafi 6angaren Fatima ni nake cutuwa aciki meyasa haka ?,is it because dan ba zan sameta bane ko me,?
_First_ ha'duwarsu da Mahmud, lokacin ba 'karamib takaici yajiba na yanda yarinyar nan ta nuna tafison kasancewa da Mahmud fiye dashi da 'kyar ya samu ya lallashi zuciyarsa akan hakan.
Then _secondly_ batun aurensu, wannan kam shiyafi komai 'kona masa zuciya saboda yanajin kamar bawai ha'din iyaye bane kamar yanda Mahmud yayi masa bayani gani yake tamkar Fatiman nason auren duk da yasan shi Mahmud 'din baso yake ba amma zuciyarsa takasa amince masa da cewa Auren na ha'di ne kamar yanda zuciyarsan akullun take bashi tabbacin cewa babu wanda zai auri Fatima akaf duniyan nan sai shi, Fateema Zahra ta Abbas ce shi ka'dai.And _now_ yayi missing kirkin Ummahn sa duk adalilin wannan banzan auren.
Haushi sosai hakan yasaka shi, yace yanzu da Ummah na nan ai da ba ruwansa da neman abinci, dan ita akoda yaushe idan ka nema toh zaka samu, ya tsani cin abincin hotel shi, yafi son cin abinci agida, shiyasa akoda yaushe yake kan hanyan zuwa gida duk da nisan da gurin ke dashi hakan besa yayi ganda zuwa aduk lokacin dayaso, abu ka'dan ke sa ya kamo hanyar gida baya yin cikakken 2 weeks mai kyau batare da ya le'ko Abuja ba, koda ba zai kwana ba ma amma in ya so sai yazo, wani lokaci dan kawai yaci abincin Ummansa ma yakoma saboda na wajen da wuri suke fita akansa bakamar na mahaifiyarsa ba.
KAMU SEDANG MEMBACA
CAPTAIN ABBAS
Fiksi UmumMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...