💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
💫 *DA BAZARMU* *WRITER'S ASS*
💫We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all........ *DAZARMU* *MUKE TUN 'KAHO*
Luv story😍
By
*Salmerh md*
*Alhamdulillah* !,
masoya. *CAPTAIN* *ABBAS* haqiqa naji dadin yanda kuka nuna soyayyar ku ga wannan littafin.hakan yasani matuqar farin ciki marar misaltuwa........kusani in sha Allahu *ana tare* 🤝*HAPPY JUMMA'AT* *2 ALL MUSLIMS* 👏🏻
*Bismillahirah manir* *raheem*
🅿 *2*
Mintina goma ya dauka agurin cin abincin,cak ya miqe tsaye
Dakinsa ya shiga ya watso ruwa yayi sallah Sannan yayi zaman shirya jikinsa da kyau.Abbas yaro ne shi amma sam bashi da wauta ko hayaniya irinta yarintan nan anatse yake komansa kamar wani babba.
Haka idan yayi gayu har mamaki zai baka don irin yadda ya iyah zama ya gyara jikinsa tsab kamar bashi ba.
Fitowa yayi da niyar zuwa gurin mummy,sai kuma yaganta a parlour tana kallon wani hausa movie.
Mummy dake zaune acikin parlourn
kallon inda taji motsin tafiya tayi,sarai tasan Abbas ne dan jiyo irin qanshin turaren dayake amfani dashi da tayi.
murmushi ne ya su6ce mata sanda ya bayyan aidanunta
Aranta ta ke jinjina irin tsabta da kula da kai da Abbas din
yake dashi.Qaraso wa yayicikin parlourn amma tunkafin yayi magana sai mummyn tariga shi dacewa
"harka shirya kenan"Murmushi yayi mata batare dayayi magana ba.
'Karaso wa yayi ya zauna agefenta
Sannan yace
"barka da hutawa mummy"Amsa masa tayi da "yauwa dan albarka"
Sannan tajeho masa tambaya tana qara kallon inda yake zaunen daga gefenta.
"Yanzu zaka miqa kudin mai fruits dinne?"
Kai Abbas din yadaga mata alamar
"ehh"cewa tayi
"Bari toh na dauko maka kudin "
tana fada ta miqe ta nufi bedroom dinta
2k takawo ta miqa masa.tare da zama a inda ta tashi dazu
Abbas. Bai kar6i kudin ba illah dariyah yayi kadan sannan yace
"Mummy inaga fah bazai wuce 1k ba kudin, dakyar ma inzai kai.
Cewa tayi kar6i de nikam Abbas ka kaimasa,idan kuma kaje da 1k din shikuma yace bai isa bafah, cewa yayi da ita "zai ma isa mummy "
Sa ke miqa masa kudin tayi tana fadin
"ungo kaje Abbas bana son musu"Kar6a yayi sannan ya juya ya fita yana fadin
"sai na dawo mummy""Uhm"
kawai tace dashi sa nnan ta maida idonta taci gaba da kallon data keyi a television.Teemah kuwa nacan bacci ne ma yadauke ta bayan fanni tamata wanka,kafin ta ahafa mata mai sai bacci ya dauke ta,ganin hakan fanni tasa ka mata pant kawai tabarta,adakin tafito taci gaba da ayyukanta.
,3:00 dot tatashi abaccin, dayake ranar alhamis ce, ba islamiyah,
shiyasa babu wanda ya damu da baccin datayin.Tana tashi kuwa dakin mummy ta fara zuwa da kwa6a66an fuskarta irin na yarinta da kuma yanayin bacci.
YOU ARE READING
CAPTAIN ABBAS
General FictionMatashi ne maiji da kansa ta kowani fanni,ya so ta so mai tsananin gaske,cikin qudirar ubangiji kuma sai bata kasance matarsa ba,sai da ta auri waninsa kafin nan,daga baya kuma kaddara ta had'a su aure............shin ko ya kuke ganin zaman zai kas...