P62

1.3K 87 2
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir rahmanir raheem*

_Before you go pointing your fingers at someone else, you may want to make sure your own hands are_ _clean............_

🅿 *62*

Da sauri yace " _ah ah Innah wannan ai 'kasa ce ta rage_ "

Bata 'dago taga me yi mata maganan ta bashi amsa da fa'din " ' _kyaleni yaro, inban kwashe duka ba 'dan waken ba isan yaran zaiyi ba hakan ma daya za'a ci ballantana kuma ya gaza haka_ "

Mahmud cikin tsananin mamaki yace
" _wai kina nufin wannan abin abinci za'ayi da shi Innah_ ?

Sai wannan karan matar ta dakata da kwasan abin da takeyi ta 'dago jin tambayar yayi matan kamar ta rainin hankali.

Tana mi'kewa taganshi tsaye kusa da ita ga wasu su biyu ma tsaye abayansa, ita tsoro ma ya bata dan yanda taganshin take tsoro ya tsarga mata azuci.

Hannun 'yarta takama tayi baya ka'dan sannan tajuya suka nufi gidansu da saurin gaske.

Wannan gidan da Mahmud yagani 'dazu nan yaga suka shiga shima sai ya biyo su abaya amma kafinma ya iso su har sun shige ciki abinsu.

Tsayawa sukayi suna 'dan dube-dube can suka hango wani matashin saurayi da bazai wuce shekara 20 ba yana kallon su daga 'dan nesa ka'dan.

Hannu Mahmud ya masa sai kuwa ya taho da sauri kamar dama jira yake su 'kira shi.

Yana iso wa ya gaida su suka amsa sannan Mahmud ya tambayi sunansa .

Matashin yace sunan sa _Rabi'u_ .

Mahmud ne yace " _yauwa Rabi'u dan Allah ko zaka mana magana da mai gidan nan_ "

Matashin mai suna Rabi'u yace " _Allah sarki ai maigidan ya kwan biyu da rasuwa, matarsa da 'ya'yansa ne ka'dai_ _suka rayuwa_ _agidan_ "

Tausayin mutanen ne ya sake shiga dukkanin azuciyoyin su har drivern taxi 'din.

Bayani Mahmud yayi wa Rabi'u akan abinda ke tafe dasu, nan take kuwa farin ciki ya baibaye ilahirin fuskar Rabi'u yafara yi musu godiya tunma be tabbatar da gaskiyar lamarin ba, shiga gidan Rabi'u yayi yai wa matar gidan bayani wanda da 'kyar ta amince da batun da Rabi'un yazo mata dashi, domin ita rayuwar yanzu tsoro yake bata, mutane sam babu tsoron Allah azu'katansu, dayawansu basa taimako saboda Allah sai dan su cuceka ko dan wani abu daban, ita kuwa da take ta  fama tana lalla6a rayuwarta da 'yan yaranta guda hu'du sam bata son wata sabuwar fitina ta 6ullo musu.

Da 'kyar Rabi'u ya shawo kanta ta yadda ta amince da su Mahmud 'din sannan Rabi'u yakoma yayi musu iso.

Su Mahmud basu tsinke da al'amarin matar ba har sai da suka sanya kawunansu acikin gidan, inda suka ga komai kamar ba inda 'dan adam ke rayuwa ba, babu komai da zai birge mutun acikin gidan face tarkace da tsummokara, Mahmud sosai ya tausaya musu jikinsa yayi sanyi 'kalau.

Rabi'u ne da kansa ya je ya janyo wata ru6a66iyar tabarma ya shinfi'da musu suka zauna akai, ganin yanayin matar ne yasa Umar yayi mata bayani abayyane cewa ta saki jikinta karta ji tsoro  sadaka suka kawo musu ba cutar da su zasu yi ba, amma intaga kamar bata yadda dasu ba har yanzun tana iya yi musu bayani sai sukoma inda suka fito.

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now