P59

1.1K 75 12
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

 
_Success means having the courage, the determination, and the will to become the person you believe you were meant to be._

🅿 *59*

Anty (mahaifiyar Mahmud) ce agaba dan haka ita ta far kutso kanta ciki, bayanta kuwa Anty Chiddy ce data bi tagama rikice wa da tunanin abinda yasamu Teemah , dan dataga ba'a bu'de mata 'kofar ba 'dazu tana barin nan gidan Anty direct ta nufa tayi mata bayanin abinda ke faruwa arikice don ita zatonta ma ko wani abu ne yasamu yarinyar shiyasa, amma Anty sai bata wani damu ba tace iskanci ne kawai ke damunta ba wani abu ba duk da haka Anty Chiddy sai da ta tattago ta suka zo tare.

Anty na shigowa tafara bin Teemah da wata muguwar harara tare da ta6e baki gefe, Teemahn na musu barka da zuwa ma amma Anty ko kulawa batayi ba tace da Teemahn" _hamsha'kiya amaryar Mahmud....., ashe kina ciki?_
da wani dirty look ta ha'da tayi maganar tata.

Jikin Teemah sosai yayi sanyi da yanayin Antyn amma duk da haka sai ta daure ranta ta 'daga mata kai cikin sanyi tace
" _ehh Anty, ina_ _nan"_
Muryarta har crashing yake lokacin datayi maganar .

Anty sai ta ta6e baki ta juya ta kalli 'kawarta tare da nuna wa Teemahn ita tace
_" wace_ _wannan awajena_ ?

_" she is your friend "_  Teemah ta bata amsa da rawar baki.

" _me na fa'da miki game da ita_ ?
Anty tasake dokawa Teemah wata tambayar tare da kure ta da idanu.

Teemah kuwa yanzun sai tayi shiru ta sunkuyar da kanta 'kasa hannayenta sar'ke cikin junansu batayi magana ba. Anty kuwa haushi hakan yabata dan haka
sai ta daka mata wani uban tsawa akanta daya matu'kar firgita Teemah sannan ta sake maimata tambayar tata ga Teenma cikin masifa.

Take idanun Teemah suka fara tara 'kwalla jikinta yafara rawa.

Anty kuwa sai ta fara kewayata tana 'kara nazarin Teemahn sannan ta wuce taje ta zauna akan cushion ta 'dora 'kafa 'daya kan 'daya kamar wata me fa'da aji..

_" Zo nan ke !_
Tasake dakawa Teemahn tsawa hatta 'kawarta se data juya ta kalleta, Teemah kuwa se ta juya tatafi ahankali ta zube akan gwiwoyinta ta zauna, ta sake yin 'kasa da kanta, tsoron Antyn yagama cika mata zuciya ayau 'din dan bata ta'ba sanin cewa 'dayan side 'din Anty haka yake ba, sosai takejin wani iri gameda hakan duk da ma bata san taka mamman abinda ta mata ba ko kuma abinda ke faruwa ba bata san wani laifi tayiwa Antyn ba, sai de tana kyautata zaton wannan arniyar ce takai 'karanta gurinta.

Anty Chiddu ma takowa tayi tazo ta zauna gefe da Anty tana idanunta akan Teemah.

Tana cikin tunanin ta tsinkayo muryar Anty na fa'din
" _har ke kin isa kinyi girman da zaki ja da maganata ko?, toh bari kiji uwar data haife ki ma bata isa tamin gadara ba domin ba'a bakin komai take wurina ba balle kuma ke......... kuma kisani baki isa kice zaki hana duk wanda yayi ra'ayin shiga gidan nan shigansa ba saboda baki da wannan damar, kinyi ka'dan, wannan da kike gani tamkar nice.......tamkar mahaifiyar Mahmud take......inajin da kaina na tako musamman nazo nayi miki bayani_ _akanta shine kuma zaki ce zaki hanata shiga gidan_ _nan?.......,_

CAPTAIN ABBASTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang