P34

1.2K 76 0
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍

HAPPY ANNIVERSARY
sis HUSSAINAH B ABUBAKAR (Mrs Abubakar)
*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Ya Allah, turn our sadness to happiness,frowns to smiles,hate to love, weaknesses to strengths, and cleanse us of our shortcomings.

🅿 *34*

Tun lokacin da Abbah ya fara yiwa Anty tsawa akanta taji duniyar ta tsaya mata cak, wani duhu taji ya mamaye ilahirin kanta har cikin k'wak'walwarta gaba d'aya, wasu abubuwan daya fad'a d'inma bata jisu da kyau ba ido kawai ta tsurawa fuskarsa yayinda yake mata masifar inka ganta alokacin zaka zaci hankalinta da nutsuwarta ta mayar akansa don ta fahimci me yake nufi da kyau, amma azahiri ba haka bane.

Anty ta kusan minti goma agurin tsaye tana tunani abin ne takeji wani banbara k'wai it seems different, kamar almara............wai yau ita Abbah ke yiwa tsawa akan abinda be taka kara ya karya ba.

Jijjiga kai tayi da k'arfi take sai tunaninta ya dawo daidai, gani tayi ba kowa agabanta ita kad'ai ce tsaye awurin, koda ta kalli gefe da gefenta ma duk haka tagani bakowa,da sauri ta juya takalli inda motar Abban ke ajiyeh sai taga wayam bakomai, alamar sun ma bar mata gidan gaba d'aya batare data sani ba tsabar yanda ta shiga zurfin tunani.

Ranta taji ya matuk'ar 6aci,wani 'kullutun daya kullera azuci ji tayi tamkar ta kurma ihu ko zai waraware, ahankali tafara d'aga k'afafunta tajuya da niyyar shiga cikin gida saboda fitar ma jitayi tafice mata arai.

Kan kujera taje ta zube sharab tamkar wata majinyaciya, sam takasa yadda cewa wannan ABBAn mahmud ne, ji take kamar an exchanging mata shi ne gaba d'aya, inkuwa wannan mutumin da kuma wannan al'amarin daya farun ya kasance gaskiya to kuwa hakika zama bai ganta ba.

Bazata ta6a bari aci nasara akanta ba matuk'ar tana numfashi,kuma nan take tayiwa kanta alk'awarin tarwatsa rayuwar duk wani mai shirin yiwa aikinta _zagon k'asa_ (khadija candy).

Tayi alwashin koda waye ke yi mata hakan sai taga bayanshi sannan wannan auren data fara magana akansan bata ga uban daya isa ya hanasa faruwa ba matuk'ar tana numfashi, ada bata d'auki al'amarin da wani girma sosai bama, saboda kawai tana tunanin zata lalla6e shine ahankali ya amince ya auri Muniran tunda ita ta nuna tana sonshi, amma yanzu ji takeyi aranta kodan abinda Abban Mahmud yayi mata ayau d'in sai ta bawa duk wani mai shirin shiga tsakaninsu kunya, sannan kuma daga baya ta kuma tarwatsa shi kamar yadda yafara had'a mata hargitsi acikin gida.

(Kunsan shi me yin abu akullum shi tunaninsa kowa ma yanayi ne, gani suke kamar duk abinda yasame su toh yi musu akayi, gaba d'aya mantawa sukeyi da k'addara)
Allah ubangiji kasa mufi k'arfin zuk'atanmu _AMEEN_ .

Koda Mahmud ya koma damaturun babu wani abinda yakeyi saboda already ya gama abinda zaiyi tun kafin yaje lagos kwanaki.

Abinda ANTY tace yayi d'in batasan yayi hakan tun kafin ta furta ba,so yanzu bawani zuwa wurin bautan k'asa daya keyi zamansa yake kurum agida, sai dai suje yawo, ko suyi karatu suje ziyara inda suka sani idan ta kama,wani lokaci kuma daddyn Teemah yajashi suyi tafiyah tare.

Yakan d'an ziyarci wajen dayake service d'in amma sai lokacin daya ga dama, kuma zuwan ma yana zuwa ne bawai dan yayi wani abu ba kawai yana zuwa ne dan ya san meke faruwa awurin kar shirun yayi yawa.

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now