P27

1.7K 95 1
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._wad'anda nasani da wanda bansani ba. 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *27*

Washe gari da safe da ya tashi sai yayi shirinsa da wuri ya fito, har kuwa lokacin daya fito d'in Teemah bata fito ba, gashi lokaci yad'anja dayake bahaka tasaba ba duk da bai fiya  yawan fitowa a irin wannan lokacin ba amma dai yasan Teemahn bata fiya makara zuwa makaranta ba.

Har zai basar kuma sai ya waske kawai ya wuce d'akinnata da niyyar tada ita, sau uku yana yana buga k'ofar amma shiru ba'a kulasa ba ganin hakan yasa kawai ya tura k'ofar yashiga ko sallamar ma bai yi ba.

Kwance ak'asa ya tadda ita tana ciccije baki tare da mammatse cikinta duk ta had'a gumi ga kuma robar ruwa ajiye agefenta.

Da sauri ya k'arasa inda take ya tsugunna " lafiya kuwa" ya fad'a yana tatta6a jikinta daga fuskarta zuwa hannunta da niyyar jin temperaturen ta, azatonshi ma zazza6i ne amma sai yaji jikin normal sai dai d'umi babu wani abu.

" meke damunki ne wai" yasake
tambayarta jin bata amsa masa tambayar farkon ba.

Ita kuwa Teemah dukda tana d'anjin ciwon kad'an-kad'an amma sai hakan bai hanata jin dad'in har cikin zuciyarta da jin muryar Abbas d'in cikin rahama  akusa da ita duk da tana tsoron hukuncin da zai mata amma tasan tana cikin wannan halin bazai ta6a yi mata mugunta ba dan duk abinsa yana da tausayi, balle yanda taga yake tambayarta cikin kulawa da k'yar ne ma idan bai manta abinda yafaru d'in ba.

Yunk'uri tayi kamar zata tashi sai yayi saurin tareta ya zaunar da ita da kyau, " ina......kwana yayah" ta fad'a idanunta na k'asa da d'an in ina saboda cikin yad'an sake murd'a mata ga kuma tsoronsa data keji.

Atakaice ya amsa mata da " lafiya " sannan ya k'ara da fad'in " wai me yasame ki ne Fateemah"

" cikina ne yake ciwo, amma nasha magani yafara raguwa ma ciwon yanzu"Teemahn ce tafad'i haka

Shikuwa tsayawa yayi yana kallonta sanda take kan maganar sai da ta dasa aya kafin ya sake cewa " wani magani kika sha"?

" ibuprofen" tabashi amsa.

" tun yaushe yafara miki ciwon"

" bayan an idar da sallah ne".

Yariga yagane meke damunta tunda shi ma atleast yayi zaman class koba komai yasan amfanin shan ibuprofen musamman ma ita da nata period d'in baya mata da wasa amma hakan bai sa ya fasa k'udurinsa akanta ba daya d'aukarwa kansa al'kawari.

Kallonta yasakeyi dakyau sai yaga tayi wata fayau da ita tamkar wacce ke jinyar satikai.

" me kuke yi a makaranta yanzu."
Ya tambayeta.

" test " itama tabashi amsa atakaice da irin sigar da ya mata tambayar dashi.

" toh yaza'ayi kenan, zaki iya zuwane?"

Kai ta d'aga masa alamar " ehh"

sai yace "okay hanzarta ki watsa ruwa sai in sauk'e ki inyaso inkin rubuta Test d'in sai mu dawo gida.

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now