P73

1.6K 104 6
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

~Dedicated to my~ ❤

*Bismillahir rahmanir raheem*

_Do not think about the past..... Accept the Present..... Think for the Future....nd face tomorrow with a sweet and beautiful smile._

🅿 *73*

Abbas a firgice ya 'dago idanunsa ya sau'ke su akan Daddy,
Daddy kam ko ajikinsa dan yana gama fa'din abinda ze fa'da ya shige ciki.

Motsi me kyau Abbas kasawa yayi sai de yabi bayan Daddy da kallo da idanunsa da suka gama riki'de wa zuwa ja, har ya shige cikin kuwa Abbas be daina kallon 'kofar ba tsawon mintina biyar kafin ya tashi ahankali 'kafafunsa ma nauyi suka masa da 'kyar yake 'daga su ya nufi 6angaren Ummah.

Zuciyarsa ce kawai ke beating da 'karfi ajikinsa bayaga haka kuwa gaba 'daya jikinsa yayi sanyi 'kalau.

Fasa zuwa wurin Ummah dan yi mata sallamar yayi kawai sai ya wuce 'dakin sa ya zauna a kujera tare da dafe kansa.

Tsawon mintina yana a haka shi ka'dai yasan me yake ji azuciyarsa baya fatan abinda Daddy ya fa'da ya kasance gaskiya, aure!......aure kuma da waye haka toh?

Yana jin wannan karan kam ba ze sake yin saken da zata ta kubce masa ba, ba ze 'ki yiwa Daddy biyayya ba amma shima zai auri za6insa koda daga baya ne.

Su Teemah ne yau a kitchen suna aikin breakfast ita da Hannah, sunayi suna 'dan ta6a hira inda duk hirar tasu Hannah ce 'kwa'kulo ta wani lokaci har fa'da sukeyi in maganar Hannah ya bawa Teemah haushi garin haka ruwan zafin jikin marfin tukunya ya zuba wa Hannah a 'kafarta.

Tare da su Ummah da Anty suka ci breakfast 'din, bayan gamawar su ne Ummah ta 'dauki na Daddy tace zata kai masa, Anty ne tace da su Hannah sukai na Yayansu ma tun da be fito an karya dashi ba, take Ummah ta hana tace abarshi yanzu akaran banza zai koro min yara na tace abari sai yazo dakan sa dan baya son ana damunsa idan yana 'dakinsa, dayake bata san da batun tafiyar sa ba.

Koda takai na Daddyn kuwa ta same shi ne yana amsa waya hakan yasa ta gama harha'da masa kafin ya kare wayar ta kawo center table ta ajiye masa agabansa, dan tasan shi be fiya cin brekfast akan dinning ba.

Yana sau'ke wayar kuwa yace mata
" ' _danki ya wuche ko?_

Da mamaki tace masa
" _wani 'dan kuma Alhaji?_

Tea cup 'din dake gaban sa ya 'dauka ya 'dan kur6a ka'dan sannan ya cire daga bakin sa ya kalle ta da kyau ya ce " _Abbas nake nufi!"_

Mamakinta kasa 6oyuwa yayi har sai da ta bu'di baki ta tambaye shi dalili dan kuwa daya zo be cemata zai koma so soon haka ba, bayaga haka ma ko sallama be je yayi mata ba haka kawai sai take jin bata yarda ya tafin ba.

Anan daddy yayi mata bayanin komai dake faruwa yace " ' _kilan haushi na da yake ji ne ya shafeki kema shiyasa har ya wuche be sanar da ke ba, amma ni kam yazo yayi min sallama da sunan zai koma bakin aikinsa ni kuwa ban dakatar dashi ba"_

Ummah kam gaba 'daya kanta sai ya kulle da maganar Daddyn bata fahimci komai ba dan haka sai tace " _Alhaji haushin ka na me Abbas zaiji kuma, ko de akwai wani 6oyayyan_ _abinda yafaru ne da_ _bansani ba_ "

CAPTAIN ABBASWhere stories live. Discover now