P76

2.2K 109 4
                                    

💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

 

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*


💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*


*Bismillahir rahmanir raheem*

_No man succeeds without a good woman behind him......either Wife or mother, if it is both, he is twice blessed indeed_🤞🏻

🅿 *76*

Haka a gida ma da yawan mutane na farin ciki da wannan aure sai faman sanya albarka akeyi.


An shirya Teemah cikin wata doguwar riga mai kyan gaske kalar touqoise blue da ratsin golden, rigar ta kama ta sosai daga 'kirji 'kasan rigar kuwa abu'de yake ba 'karamin fito da kyaunta rigar tayi ba.

Hannah kam yau ba  ta jin gari, tunda aka 'daura auren ta fara 'kiran Teemah da suna _amaryar_ _Yayah_ , Teemah tun tana mitar bata so har ta ha'kura tayi shiru balle da taji kanta yafara sara mata ai tuni sai ta nemi 'dakin da aka sau'kar da Mummy ta shiga da niyyan hutawa.

Mummy kam korota tayi tace maza taje cikin 'yan uwanta ta zauna bata son zama shirun nan.

Fuskar shagwa6a tayi tace
" _Allah Mummy kaina ke ciwo ne shi yasa_ "

Mummy tace taje yanzu ta 'dau maganinta tasha ba jiya an siya miki magunguna ba, hayaniya ne ke saki ciwon kan ba komai ba.

Fita tayi taje 'dakin su nan ta samu Hannah da 'kawayenta sai ihu sukeyi, haka ta zauna agefensu tayi shiru bata kula su amma duk yadda Hannah tasan zata takalo ta tasata magana sai tayi.

'Karfe uku nayi duk suka wuce gidajensu da sunan zasu je kowa ta yo shirin walima su dawo.

Hannah ma kasuwa ta shiga aka bar Teemah ita ka'dai.

Taji da'din raguwar hayaniyan amma kuma sai ta ringa jin zazza6i na son taso mata.

Zama tayi a'dakin nasu ta'ki zuwa ko'ina kuma ta'ki shan maganin ma .

Kafin yamma kuwa zazza6in Teemah sabo fil ya dawo ga jiri dake faman  'diban ta har bata iya tsayuwa da kanta sai ta kama abu, gaba 'daya ta fita a hayyacinta.

Anty ne tazo neman ta dan afara shirin yi mata kwalliyar yamma ta zuwa walima, gagarumin walima ne da Daddy da kansa ya shirya shi.

Sosai Anty ma tayi 'ko'kari dan kuwa duk wasu kaya da Fateemah tayi anfani dasu da ma wa'dan da zata sa agaba duk Anty ne ta 'dau nauyin yinsu tare da 'dauko wata  shahararriyar mata wacce ta 'kware a fannin kwalliya na zamani domin ta ringa yiwa Teemah make'up har biki ya 'kare.

Ko yanzun ma da kanta ta shiga duba Teemah sai ta tarar da ita kwance ta du'kun'kunu a cikin blanket.

Da sauri ta 'karaso tazo gareta tana tambayar ta "me ya faru?

Tayi saurin fahimtar abinda ke faruwa ne sanadin zafin da taji jikinta yayi ga kuma ha'duwan da ha'koranta keyi.

Fita tayi da sauri da niyyan 'kiran Mummy sai kuma tariga ha'duwa da Ummah tun kafin ta kai ga Mummyn.

Ummah kam ganin hankalin Anty atashe yasa tayi saurin barin maganar da takeyi ta taho ta tareta da tambayar meke faruwa ne?

Bayani Anty tayi mata atakaice tun kafin tadasa aya kuwa Ummah ta furta " _subhanallah_ " sai tayi gaba, tare suka 'dunguma zuwa 'dakin su Teemahn da Anty da wasu mata guda biyu.

CAPTAIN ABBASحيث تعيش القصص. اكتشف الآن