1

54.2K 2.2K 131
                                    

Bilyn Abdull ce🤙🏻

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ*

Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

Ya rabbi ka bani ikon faɗar abinda zai amfanar da al'ummar MANZON ALLAH (A.S.W), ka tsare harshena da alƙalamina ambaton abinda zai cutar da ni da ku a duniya da lahira.😭🙏🏻

Ya ALLAH ka gafartama mahaifina masoyina da dukkan al'ummar musulmi da suka rigamu kwanta dama, ALLAH ka kawo mana ƙarshen wannan annoba ta corona virus (covid-19), domin rahamarka garemu😭🙏🏻.

_____________________________________
BOOK ONE
Shafi na ɗaya
_____________________________________

...........Ko wacce kafar yaɗa labarai da ta yanar gizo labarinsu a wannan safiya ta laraba shine sace shahararren mai arziƙin nan *Alhaji Sadi kokino (ba giyar yaro ba)*.
A yanda labaran ke ta yawo an sace Alhaji Sadi kokino ne a daren jiya talata a filin jirgin sauka da tashi na babban birnin ƙasar. Abu mafi ɗaure kai ga wannan lamari shine ta hanyar da mutumin da yay garkuwa da shi ya ƙwamushe sa. Da yawan mutane da suka shigo jirgi ɗaya da Alhaji Sadi kokino sun tabbatar ma jama'a da lafiya lau ya sauka, harma ya gaisa da wasu tsirarun mutane da suka je tarbarsa. Sannan akwai wasu ƴan jarida guda biyu a filin jirgin da har suka ɗauki hotansa da gajeren bidiyo. Kowa ya shaida Alhaji Sadi lafiyar ALLAH ya shiga motar da ɗaya a masu gadinsa ya buɗe masa, sannan amintaccen direbansa yaja motar a gaban kowa. Sai dai a lokacin da motocin suka shiga harabar gidansa aka sake buɗe masa ƙofa dan ya fita sai yace ku ɗaukeni inda kuka ajiye, a taƙaice dai Alhaji Sadi kokino yayi ɓatan dabo a hanyar dake tsakanin filin jirgi zuwa gidansa.
Zuwa yanzu dai jami'an tsaro sun bazu ta ko ina nemansa, tare da buɗe kunnuwa da idanu ko za'aji wani abu da ga bakin wannan mai ƙwamushe da ba'a san ta yanda yay siddabarun sace Alhaji kokino ba...

*____________________________________*

A yayin da masu yawun mai da yanda akayi ke kaikawo akan wannan ruɗaɗɗen labari suma talakawa ƴan bani na iya sai tofa nasu albarkacin bakin suke. Ko wane dandalin sada zumunta na yanar gizo ka shiga sai kace nace akeyi. A yayin da wasu ke jimamin lamarin wasu ALLAH ya ƙara suke faɗa, a wani gefen kuwa ma kai tsaye suke ƙaryata lamarin da dangantashi da farfaganda irinta manyan ƙasa ce kawai, ƙilama yana can kwance a gidansa lafiyar ALLAH.
Daga masu ƙaryatawa har waɗanda suka gaskata kowa yana da dalilinsa, dan kuwa a yanda ƙwamishen ya kasance dolene ya bada mamaki, musamman idan mukai dubi da jami'an tsaro da cctv cameras da ke zagaye da filin jirgin, ga haske ta ko ina tamkar rana.

Koma dai yaya abin ya faru lokacine zai bayyana mana hakan😟.

*___________________________________*

Kwance yake a bayan motar idanunsa a lumshe tamkar mai barci, lokaci-lokaci yakan ɗanja guntun tsaki tare da huro zazzafar iska daga bakinsa.
Duk da kasancewarsa gwarzo kuma jarumin mutum mai ƙoƙari da jajircewa a aikinsa kallo ɗaya zakai masa a yanzu ka hango tarin gajiyawa da ɗunbin kasalar dake tattare da shi.
Tsayuwar motar da buɗe murfin da akayine ya tilasta masa buɗe lumsassun idanunsa kaɗan tare da ɗago hannunsa ya kai dubansa ga agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannun, kaɗan ya yamutse fuska yana sake huro iska kaɗan kafin ya sauke hannun da maida dubansa ga ƙofar motar da aka buɗe.
Tamkar bazai motsa ba sai kuma ya yunkura a hankali ya ja baƙar rigar sanyinsa jibgegiya dake gefe ya zura kafafunsa waje.
Da sauri wanda ke tsaye a gabansa da alama shine ya buɗe ƙofar yay azamar kai hannu zai amshi rigar sanyin yana sake ƙamewa alamar girmamawa.
Kansa ya girgiza masa ba tare da ya bashi rigarba, ya matse idanu kaɗan saboda sara masan da kansa yake na azabar ciwo, ya sauke numfashi kafin ya fito gabaɗayansa yana tura ƙaramar bindigar hannunsa a aljihun bayan wando.
Idanunsa da ke jajir ya ɗago yana saukewa akan matasan samari biyu, cikin hanzari suka ƙame tare da sara masa. Hannunsa na dama ya dinƙule kawai yay gaba ba tare da suma yace musu uffan ba. bishin sa sukayi a baya suma ba tare da sheresun da yay ya damesu ba.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora