RAYUWA TA PRT 1 PAGE 1

132 6 2
                                    

_BISMILLAHI ARRAHMAN ARRAHIM_

*RAYUWA TA THE NOVEL*✍🏽📔

_Page 1_

'''Kamar yadda Kuka Sani Mutane mabanbantane a wannan duniyar da muke ciki.

Kuma kowane mutum da irin nasa halin, ko dabi'a,

Wannan Labari ne Akan wasu Matasan 'Yan uwa su Uku wanda suka hadu a kan soyayyar Mace guda daya Tallll.

Kafin Sanin Matasan yakamata kusan Iyayensu, da kuma mahaifiyar Iyayensu.

HAJIA RABI'A DAN BATTA Macece 'Yar kasuwa wadda ta tara makudan kudade don ganin tasa yaranta cikin rayuwar daula da farin ciki.

HAJIA RABI, Tanada Kudade masu sunan kudade inda Takeda yara guda Hudu.

1. ABDUL RA'UF SANI DAN BATTA.
2. ABDULLAH SANI DAN BATTA.
3. ABDULMUMIN SANI DAN BATTA.
4. FATIMA SANI DAN BATTA.
    Wadannan sune 'ya'yan Haji Rabi, Acikinsu Ra'uf ne Babbah.

Suntaso kansu a hade ne domin kuwa Uwarsu daya kuma ubansu daya.

Hajia Rabi Ta baiwa kowannensu daga cikin 'ya'yanta Jari wanda ya fara kasuwancinsa dashi.

Idan taga kokarin ka saita kara maka jarin, Ahaka rayuwar 'ya'yanta suka cigaba da kasan cewa.

Harma suka koma gasar wanda yafi iya kasuwanci don cigabansu, Abdallah shine na biyu Halinsa kam dai ba irinna sauran bane.

Domin Abdallah na dabanne, Akomai Yakan fara duba kansane kafin sauran 'yan uwansa.

Ahaka Suka cigaba da rayuwa har Allah yasa sukakai munzalin aure Hajia Rabi ta aurar dasu dukansu.

   Bayan Sunyi Aure, Kowanne Allah ya Azurtashi da san taleleyen yaro.

Fatima wadda itace karama a cikinsu Itama sai Allah ya bata 'ya mace.

Wanda itama ta auri mijin ta mai kudin gaske.

Ra'uf Ya haifi yaronsa mai suna ABDULLATEEF.

Abdallah Ya Haifi Yaronsa Mai suna ASLAM.

Abdulmumin Ya haifi yaronsa mai suna KHALEED.

Fatima ta haifi 'yarta Mai sunan
YUSRAH Amman ana kiranta da (Suhailat) saboda sunan Mahaifiyar Baban Tane.

  Haka rayuwar Wadannan yara Tacigaba da kasancewa.

Hajia Rabi Tasamu ta gina Ahalinta tinshekarun baya, Bayan mutuwar mijinta.

Tayi aiki tukuru don ganin Ahalinta yaci gaba.

Haka zalika yaran ma kansu a hade yake da kuma iyayensu mata da maza.

Suna rayuwarsu ta farin ciki, Aslam shine wanda ya dauko halin mahaifinsa.

Domin kuwa shi kamar mahaifinsa yake bayason rainin wayo dana hankali.

Koda suna Yarama shine yake fitowa a boss domin kuwa bayasan wasa da daria da yawa.

Haka yake kuma halin mahaifinsa kenan koda yana yaro.

Amman hakan bai hanasu cigaba da rayuwarsu cikin farin ciki ba.

Kafin Shigowar Wata Yarinya Guda daya Tallll, data Raba kan 'yan uwan.
..........

Sunanta NADIYA. Yarinyace 'yar budurwa haka, Nadiya Tanada matukar Kyau sosai mara misaltuwa, Mai karatu idannace kyau.

Hmmm Ina nufin Da za'a hadata da kyau aga wayafi kyau, tofa lallai kyau guduwa zaiyi domin yasan tafishi kyau🥰

Gata Fara kamar 'yar fulani, Gata da Gashi.
Nadiya tana rayuwa ne a gidansu masu matsakaitan Karfi.

Mahaifinta Ya manyanta gashi bayada ishashshiyar Lafia, Yau baki gobe tsumma.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now