RAYUWA TA PRT 2 PAGE 9

4 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*✍🏽📔

✨ _PART 2_ ✨

9️⃣

'''DA DADDARE.

GIDAN ALHAJI ABDULLAHI.

Nadia ce kwance gaba daya batajin dadi.

Aslam ne ya shigo Dakinta,
Zama yayi ka stool inda yace Nadia!

A tsawan wannan lokacin babu abinda kikeso irin kiga Ahalinki baki daya.

A koda yaushe kikance yaushe zakiga 'yan uwanki da Maman ki.

Meyasa Dama yazo miki na komawa garesu kike gudun hakan?

Nadia ce cikin sassanyar murya tace Aslam ba banaso komawa wa 'yan uwana bane.

Saidai banaso na tafi na barka,
Gani nakeyi idan harna tafi zakayi aurene ka barni.

Hmm Nadia kenan waya fada miki cewar idan kintafi shikenan na barki...

Kisani tafiyar kine zai kara mana kusanchi ma.

Domin saikina wajen Ahalin kine Daddy na zaije ya nemamin aurenki.

Sannan Daddy yace Ana Maidake gida Za'ayi maganar bikinmu.

Nadia Kwayar idon Aslam din ta kallah Inda tace Kayimin Alqawarin zaka aureni.

Koda wane irin kalubale zaka fuskanta.

Nikuma nayi maka Alqawarin zan aureka kodama ace an badani wa wani.

Aslam a baya banida buri irin Hankalina Ya dawo jikina na tina komai daya faru dani a baya.

Amman yanzu banaso na tina komai sonake na kare RAYUWA TA da kai gaba daya.

Babban Abin tsoro na kada na tina komai Kuma ya kasance inada Miji

Nadia ta fadi cikin damuwa.

Aslam rike hannun Nadia yayi sannan yace Nasan kowace ke.

Kuma sani cewar bakida Miji ke Budurwace kamar sauran 'yan mata.

Nadia yanzu ko Nusaiba bazaki iya tinawa ba?

Aslam Wace Nusaiba?

Shiru Aslam yayi.

Sannan yace Nadia Nusaiba Aminiyar kice, Kunyi kawance da ita tin kuna yara.

Tafi karfin Aminiya a wajenki itadin kawarkice.

Kina matukar santa sosai saboda takan sanar dake Gaskia duk dacinta.

Kina daukan Shawarar ta, kina kina matukar kaunarta kema.

Nadia Cewa tayi Nidin?

Eh kwarai kedin Nadia,

Zanso Na ganta Aslam Domin yadda ka fadeta lallai kasanni da ita.

Girgida Kansa Aslam yayi sannan yace Zaki Ganta Nadia.

Zaki ganta nan bada dadewa ba inshaAllah zankaiki gareta.

Kinaji kisamu ki kwanta kiyi bacchi yanzu.

Zuwa da Safe saimu karasa maganar koh?

Cikin shagwaba Nadia tace Ni banajin bacchi kawai kazauna a nan...

Ke Daddy na baisan na shigo nan ba sokike ya shigo ya kamani.

Idan ya kamani me zance masa?

Kace kazo wajen matarkane!

Hmm kece kikasan hakan shibazai fahimta ba shekeni zaiyi.

Nadia Kam dai kawai shiru Tayi idonta ya kada yayi jajawur.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now