*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖
'''🅿️ART 3️⃣'''
*PAGE 2️⃣*
'''GIDAN ALHAJI BASHIR.
Nifa banga abinda zaka fadamin ba Aslam.
Babu wata magana tsakanina da kai...
Suhailat kinsan meyasa tsawon wannan lokacin raina bai baci ba akan duk abinda kikemin?
Suhailat ke 'yar uwata ce bazan canja hakan ba.
Sannan duk abinda ya faru Suhailat banada zabi ne akan hakan.
Suhailat kihango faruwar haka a tattare dake abinda ya faru da Nadia.
Nadia bayan duk wannan abin daya faru da ita babu wani wanda tafi son kasancewa tare dashi irina.
Suhailat Nadia ta kaunaceni wanda ya kai ya kawo Tare muke zama muyi Komai.
Shin Suhailat kifadamin Ya kamata na guji Nadia a lokacin da ta nunawa duniya cewar nine wanda tafiso.
Shinnayi mata Adalchi kenan ita tana bukata ta nina nuna bana bukatarta?
Suhailat ke macece mai tausayi,
Kiyi tinani idan da kene hakan ta faru shin saina kyamaceki saboda kin sami wannan lalurar?Sam bazanyi hakan ba Suhailat.
Na Amince da Nadia ne don Banason tashiga wani hali idan harta gano cewar Banida Ra'ayi a kanta.
Suhailat ki fuskanceni, Kin taba tambaya ta shin inada zuciya a kirjina?
Shin Nasan me mutum yakeji idan yana son mutum?
Suhailat banbaki Amsar wannan tambayar taki ba.
Kuma har a yanzu banida Wannan Amsar saidai Nasan me mutum yakeji idan aka gujeshi musamman idan yana bukatar aka sance tare dashi.
Aslam tashi yayi daga kan kujerar sa ya dawo ta Suhailat sannan yace Dan Allah Suhailat.
Ki fuskanceni dakuma inda na Dosa. Wallahi Inajin tausayin Nadia sosai.
Kuma bazan iya rabuwa da itaba a halin da ake ciki!
Suhailat cike da kishi tace Aslam shiyasa nace kayi rayuwar ka nima nayi tawa.
Aslam A halin da ake ciki kasancewar mu a rabe zai fi mana alkhairy.
koda din cen ba lokaci kake bani ba.
Saidai naje gidanku badai kai kazo gidan mu.
Baka kirana a waya saidai na kiraka a waya.
Baka turamin da kalmar ina sonki ta haka kawai saidai na tura maka.
A koda yaushe baka tinawa dani nice kadai nake haukana Daman.
Kidena fadin Haka Suhailat duka yanzu zangyara.
Zandinga kiranki a waya, sannan zan dinga zuwa ganinki indai har hakan zai faranta miki ranki.
Nidai banason kasancewarki cikin kunci don Allah.
Suhailat kallan Aslam din tayi sannan tace Wannan itace dama ta karshe da zan baka.
Aslam idan har nakara samin tangarda a tattare da kai.
Tabbas zan rabu da kai na har Abadah kuma kasani koda Daddy da Mommy bazasu fadamin naji ba akanka!!!
Aslam wani dum dum yaji a zuciyarsa.
Domin kuwa burmata ya karayi!
Shikenan babu damuwa na yarda da hakan Suhailat yanzu kiyi murmushi!
Katashi ka tafi.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
Fiksi UmumLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?