*RAYUWA TA THE NOVEL* 📔📖
_( My Life )_'''PART SIX'''
*PAGE 7️⃣*
'''PRIVATE HOSPITAL.
Meyasa Haka? Nifa Lafia na Qalau Lateef.
Raheelah da Radeeyah ne A Asibitin da Ammie take.
Lateef ne hankalinsa ya tashi, Gefe kuma Khaleed ne da Suhailat Sai Aslam.
Ai Ammie Duka Hankalinmu ya tashi Raheelah ko gida basuje ba nan direct mukazo.
Allah sarki, Bawani Abu bane Jini nane kawai ya hau shine kawai.
Lateef sauke numfashinsa yayi da cewa Allah ya kara miki Lafia Ammie.
Khaleed ne cikin wasa yace Kinfa tsufane kawai Ammie cikin tsokana.
Bawani nan Na tsufa ai kafini tsufama, Cewar Ammie cikin wasa.
Suhailat ce zaune kan Gadon kusa da Ammie.
Yanzu Ammie ki huta zamuje waje kada mudameki.
A ah To ai sainafijin dama dama idan kuna nan, Amman Amm, Bari Azo a kaiku gida ma kawai saboda Ga Lateef ma ko Uniform bai cire ba.
Mahaifin Lateef ne yashigo, RAUF.
Bayan yin sallama.Amm, Munyi magana da Doctor dinma. Yace ba wani abu bane kawai jininne yadan hau.
Amman ba matsala bane, Yake Muje kisamu fruits kisha kihuta.
Ammie cewa tayi thom babu damuwa, Raheelah da Radeeyah ne Zasu tafi don driver dinsu yana jiransu.
Allah ya kara sauqi, Sukayi Sallama da Ammie suka fito.
Lateef ne yace Ammie zan rakasu ina dawowa.
Fitowa Yayi Ya biyo su Raheelah din wanda duka suke sanye da Uniform a jikinsu.
Nagode Raheelah, Murmushi Raheelah tayi Haba Karka damu Idan bamuyi maka haka ba wa zamuyiwa?
Radeeyah murmushi tayi masa da cewar Karka damu Lateef ai yima kaine.
Rakasu Yayi har wajen Motar su.
Sukashiga suka nufi izuwa gidansu.
Toh Yanzu ya Kamata ace Amm Abdul RAUF Suntafi su Khaleed.
A ah Ammie nifa tare dake zamu tafi, cewar Khaleed.
Nima tareda Ita zantafi Suhailat ta fada, Lateef shigowa yayi.
Me akecewa ne?
Wai nace duka kutafi gida shine sukecewa tare dani zasu tafi.
Lateef dinma cewa yayi Ai Ammie Nima tare dake zantafi gida.
Dariya tayi da fadin, Kaima?
To ai shikenan..Abdul Rauf Katafi da Daya motar Su zamu tawo dasu da Mustapha.
Thomm Babu damuwa Ammie cewar Mahaifin Lateef din.
GIDAN SU RAHEELAH.
Hankalina Duka Yabi ya tashi Wannan wane irin sanin ya kamata ne?
Baba kuma kaima da hankalin ka kabiye musu kuki dawowa da wuri?
Kayi hakuri Alhaji Munje Asibiti ne Dan Ajinsu ne Aka kwantar da Mahaifiyar sa shine.
Mukaje na kaisu, Shin waya bada ikon Aje Asibiti? Wannan Yaronne ko?
Shin Raheelah Meyasa bakyajin Magana ne wai?
Saunawa zan fada miki Akan cewa banason Ganinki da wannan yaron?
Shin kinzata duk abinda kikeyi bansani ba?
Kallanki kawai nakeyi, Duk boye boyenki.
Shikenan Zan canja muku makaranta inyaso sai muga, Abinda zai faru,
Mahaifiyarsu tana Gefe batace komai ba tayi shiru.
Raheelah Kallan Radeeyah tayi.
Alhajin fita yayi sannan ta kirasu da cewa meuasa bakwajin magana ne?
Kunfison koda yaushe mahaifinku yayita muku fada?
Mamie ba haka bane, Ammie cefa batada lafia shine mukakai Lateef din shikuma daddy yanzu yake fada.
Shikenan to daga yanzu kudenayin abu da kanku kudinga sanar dani kunjiko?
Thom Mamie cewar Raheelah da Radeeyah.
BAYAN WASU KWANAKI.
Lateef ne yazo Gidansu Raheelah a Motar Gidansu.
Mahaifin Raheelah ne yazo fitowa da Motarsa inda ya ganshi a tsaye.
Fitowa yayi, Kai waishin Banhanaka Kula Raheelah bane?
Na canja mata makarantar ma bazaka rabu da ita ba?
Kaga 'yata Karatu nakeso tayi yanzu ba soyayya ba.
Shin nawa Raheelah take da har zaka takura mata da wata soyayya?
Daddy kayi hakuri,
Kull niba Daddyn ka bane, Kajiko?
Kuma inaso karabu da ita..Idan har Kai Iyayenka basu damu da kaiba toni na damu da 'yata.
Tinda kai soyayya aka turakayi Makaranta.
Kuma katafi kabar Kofar gidannan kafinnayi maka babu dadi kaji na fada maka.
Lateef shiru yayi bai tankawa Mahaifin Raheelah ba Amman Yaji matukar Bakin cikin Maganganun da ya fada masa.
Mota Lateef ya shiga yatafi da niyar bazai kara kula Raheelah ba.
Saboda kausasan Alhaji a gareshi.
WASHE GARI.
Kiran Raheelah ne yashigo wayar Lateef,
Kindagawa yayi domin ya tina Maganganun da mahaifinta yayi masa.
Cen Sakon Tane ya shigo wayar sa.
Shima bai duba ba...
WASHE GARIN WATA RANAR...
GIDAN SU RAHEELAH.
Alhamdulillahi!!! Wannan Abune dana dade ina nema subani.
Yanzu shikenan zanbar wannan takaicin danake ciki na rashin samin lokacin iyalai na.
Mahaifin Sarah ne, Shida Mahaifin Raheelah Suna Magana.
Yanzu Cen Kasar London din zaka tafi?
Ehh Zan koma cen Saboda gaskia cen din zaifimin saboda ayyukan duka sun koma cen din.
Toh Amman Karatun yara fa da sukeyi ya zakayi dasu?
Ehh Gaskia tare nakeso mutafi dasu, Saboda banason barinsu a nan hankalina zai rabu.
Kuma ta bangaren mahaifiyarsu fa dangane da tafiyar?
Ehh babu wata matsala jiya munyi magana da ita na sanar da ita kuma ai tasan yanayin aikin dama yau ana cenne gobe anacen.
Gaskia ne.
Hakan Yayi, Allah ya bada Sa'a, inkaje sai yaushe zaka dinga zuwa nan kenan?
Ehh Kamar dai Hutu haka yara zasu dinga zuwa amman ni saboda yanayin aikin.
Zan iya zuwa koda sau dayane a shekara inshaAllah.
Well Babu Komai, Hakan yayi, Allah ya bada ikon yin hakan,
Ameen Thumma Ameen.
Wayar Lateef ce take ringing Dagawa yayi.
Radeeyah ce take fadin, Lateef Raheelah Batada Lafia Dan Allah Kazo Sunanka take fadi.
Lateef hankalinsa tashi yayi, Meyafaru da Raheelah Fadamin Radeeyah.
Lateef tinjiya kaikadaine take fadin sunanka, Daddy Yace ta rabu da kai, Tana cikin Matsala Dan Allah kazo ko hankalinta zai kwanta.
Lateef Shiru Yayi, Kafin yace tana ina??
Yau Zamu tafi Lateef Idan bakazo ba, Shikenan Rayuwar Raheelah tana cikin damuwa.
Lateef hawaye ne ya zuba a idonsa.
Zuciyarsa cike da Kunci.
'''_WRITTEN_
_BY_
_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
Fiksi UmumLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?