RAYUWA TA PART 5 PAGE 10

6 1 1
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖

'''PART FIVE (5)'''

*PAGE TEN (10)*

'''GIDAN SU NUSAIBA.

Ke Kinsan Ina Kaunarki Nusaiba.

Amman meyasa kikeson matseni akan wannan Maganar?
Salman ne shida Nusaiba.

Duk Abinda ya faru ya rigada ya faru kayi hakuri nayi laifi kuma tabbas bai kamata ba.

Nasan cewar kai mai fahimtane a ko wane lokaci.

Salman Shiru Yayi Mata,
Yariga ya wuce.

Domin gujewa hakanne ma yasa na sanarwa da mahaifina.

Kuma Zuwa cikin wannan satin za'azo za'ayi maganar aurenmu dake inshaAllah.

Nusaiba wani irin dadi taji a zuciyarta.

Alhamdulillah take fadi a zuci,
Naji dadin wannan Maganar taka.

Kuma na gode da fahimtata da kayi Salman.

Hmm Nusaiba dole na fahimceki saboda ina sonki.

Kuma banason rasaki.

Domin kada wani ya kara dawowa shiyasa zanturo idan Anyi magana anbani ke babu wani wanda zaizo da wata magana daga baya.

Hakane. Cikin murmushi Inji Nusaiba.

Wayar tace tayi ringing dubawa tayi.

Hello, Subhanallahi Thom Ganinan Zuwa.

Meyafaru?

Wai Nadia ce take Asibiti Ankwantar da ita Umman suce ta kirani.

Tohh Subhanallahi! Ai bakyaje ke kadai ba muje mana.

Nusaiba cewa tayi ok Barina shiga gida na sanar da Umma Sai mu tafi.

PRIVATE HOSPITAL.

Ammie ce Itada Umman Nadia da Kuma Mustapha Driver.

Doctor ne yace wa Ammie, Hajia inason Ganinki Don Allah.

Ammie cewa tayi babu damuwa, Wannan ce mahaifiyar ta itama zata iya zuwa?

Babu damuwa bismillah inji doctor.

Shiga Office dinsa sukayi suka zauna.

Hajia wannan ba wata babbar matsala bace karku daga hankalinku.

Nadia tana dauke da Juna biyu!

Ammie kallan Umman Nadia tayi Cikin Fara'a.

Amm! Kuma Yawan Stress ne haka yakedan damunta.

Tasaka Lamarin Aslam a ranta sosai wannan shine yaja mata Jiri harta fadi.

Amman inshaAllah yau ma zan Sallameku ku koma gida.
Nasaka Mata drift idanya kare saiku tafi da ita.

Saidai ta dan cire damuwar koyayane daga zuciyarta.
Asamu a dinga debe mata kewa kar a dinga barinta ita kadai tana tinaninnika.

Domin hakan zai iya kawo wata matsalar kuma daban.

Alhamdulillah! Umman Nadia ta fadi Ashe dai Zanga jikana.

Ammie Cewa tayi Doctor Mungode kwarai da gaske

Yanzu ya ita Nadian Ya jikinnata zamu iya ganinta?

Ehh Dayake yanzu dai munyi mata allurar bacchi.

Saboda bata samin bacchi mai kyau, So tana bukatar ta huta sosai.

Kubarta ta huta idanta tashi saina rubuta sallama inshaAllah.

Thomm shikenan Babu damuwa Doctor.

Ammie tashi tayi suka fito.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now