RAYUWA TA PRT 1 PAGE 2

45 0 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*✍🏽📔
    
_Page 2_

'''RA'UF HOUSE.

Lateef ne aka bude masa gate ya shigo da motarsa,

Kanwarsa Da Batafi shekara Sha 17 bace zaune garden tana karatu.

ELHAM: Yaya Sannu da Zuwa.

LATEEF: Yauwa Elham,

Tana zaune tana karatun Textbooks.
ELHAM: Naga Abokin ka yazo tindazu  Yake jiranka.

LATEEF: Husshhh!! Hakane Na manta wallahi yanata jirana da sauri Lateef ya shiga cikin Parlourn gidansu.

Abokin sane zaune Kan kujera,

SALMAN: Kaiya rayuwarka da haka Malam? inata jiranka ka ajiyeni.
Fadar Abokin Lateef wato Salman.

LATEEF: Sorry Mutuminah Sorry!!!! Ai nasan zaka fahimceni, Wallahi Natawo Kuma wani dan uzuri ya maidani baya.

Wallahi Wata Yarinya ce nakai Asibiti,

SALMAN: Kaiiii!!!! Mekake cewane? Jiya kagama cemin banda Kanwarka mahaifiyarka babu macen da take shiga motarka.

LATEEF: Kaga Aibaka tsaya na gama baka labarin ba koh?

SALMAN: Shikenan inajinka.

LATEEF: Yauwa Toh Bayan Nayi waya da kai na tawo wallahi shine na ganta a bakin titi.

Tana kuka haka, to kuma mace ace tana kuka kaga abin a tambaya ne?

Na tsaya na tambayeta, Mahaifin tane bashida Lafia ta tsaida abin hawa duk sunki tsayawa.

Wallahi Tabani Tausayi sosai, shine kawai nace muje ni in kaisu Asibitin shine fa mukaje cen gidannasu Muka dauka mahaifinnata.

Sannan kuma nakaisu Asibitin, shine na tawo.

SALMAN: Sannu da Kokari, Malam Abdul Lateef, Kaikam indai taimako ne.

Yadda kake taimako Kaima Allah Ya taimaka Maka Fadar Salman.

LATEEF: Ameen ameen Mutuminah.

SALMAN: Yanzu muje,

LATEEF: Afuwan Motan ya baci amman zanyi waya azo a kaita wajen wanki inyaso zan dauki wata kawai koh?

SALMAN: Ehh hakane, to Yanzu kajirani Indan nayi Wanka inyaso saimu fita gaba daya tinda dama zan koma wancen asibitin ma.

SALMAN: Shikenan Jeka fito, inji Salman.

PRIVATE HOSPITAL.

Nadia ce itada Umma a cikin dakin da Mahaifin su yake.

NADIA: Umma Ina zuwa Ina tinanin Nusaiba tazo barinaje nazo da ita.

UMMA: Thomm Nadia,
Nadia fitowa Tayi farfajiyar Asibitin.

NADIA: Ashedai zaki gane Fadar Nadia.

NUSAIBA: Hmmm Kekuwa saikace yauna taba zuwa Asibitin,

Ni mamaki ma nayi yadda kika haddace Lambata kika kirani keda baki irin wannan haddace haddacen.

NADIA: Nusaiba kenan Ai tin lokacin da kikacemin ya kamata nasamu na haddace koda Lamba daya ce tin lokacin.

Na haddace lambarki saboda bansan abinda zai tashi ba.

NUSAIBA: Hmm lallai kuwa towa yabaki waya kuma?

NADIA: Nusaiba ai Labarin ne yanada dan tsayi muje ku gaisa da Umma dai.

Mufito saina fada miki cewar Nadia.

Garzayawa sukayi zuwa cikin Dakin da Baban Su Nadia Yake,

Nusaiba durkusawa tayi ta gaisheda Umma.

NUSAIBA: Ya jikin Baba kuma?
UMMA: Da sauki Nusaiba.
NUSAIBA: Allah Ya kara sauki Umma.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now