RAYUWA TA PRT 2 PAGE 5

13 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL ✍🏽📔*

✨ _PART  2_ ✨

5️⃣

'''HOSPITAL.

Ammie ce A Kan Khaleed,
Mahaifiyar sa Da Mahaifinsa Suna Tsaye.

Suhailat kuka takeyi.

Aslam da Lateef suna Tsaye suma.

Nusaiba da Yaya Nooratu ne suma a gefe.

Wai Shin waya bashima damar daukan yarinya a mota waya bashi wannan damar?

Akanme zaije gidansu ya dauketa.

Lateef ne yake fada ransa a bace.

Haka yace Ammie ce tace yazo ya dauketa.

Ya kaita gidanta zasuyi magana.

Toyanzu ga irinta nan Ninasan Khaleed ba magana yakeji ba.

Tare suka fito yanzu shi anganshi ita kuma ba'a ganta ba.

DPO ne yashigo dakin bayan Yayi sallama.

Yauwa Dpo me ake ciki yanzu?

Abdul Lateef ka kwantar da hankalinka kaji koh.

Har izuwa yanzu bamu sami wani abu da zai nuna mana cewa Dauketa akayi ba (kidnapping)

Kokuma wasune suka dauketa suyi mata magani.

Ahalin yanzu bazamu ce komai ba dole sai Khaleed ya farfado tukunnah domin muna bukatar bayanai daga gareshi.

Ammie ce ta kalli Dpo din.

Dpo duk yadda za'ayi adawomin da yarinyar nan ayi.

Tabbass ina bukatarta kuma a raye ba amace ba.

Mune gatanta Dpo idan har yarinyar nan ta salwanta Bazamu yafema kanmu ba domin duk abinda ya faru da ita laifin mune.

Ammie kidena fadin hakan babu saninki domin da Khaleed ya fada miki bazaki barshi ba.

Mahaifiyar Khaleed dince ta fadi haka.

Ashe shiyasa yacemin yana bukatar kudade kenan? Nace yaje ya karba.

Kungani laifin kane ai Abdul Mumin akanme zakace yaro yaje ya karbi kudade haka a kamfani.

Toshikenan yanzu ansamu kudin sundawo shima ya dawo amman 'yar mutane bata dawo ba.

Dpo Dole ne fa Kusamo yarinyar nan Nadia.

Insha Allah Hajia zamuyi iya bakin kokarinmu wajen ganin ta dawo.

Kuyi hakuri kunji inshaAllah Nadia zata dawo.

Inaji a jikina a duk inda take tana cikin kulawa.

Nusaiba ce tace thomm Ammie.

Zan bada mota yanzu a kaiku gida ku kwantar da hankalinku.

Sannan kubama Mahaifiyar ta hakuri a madadina kafin nazo.

Ehm Aslam kiramin Mustapha yazo ya kaisu gida.

Thom Ammie cikin biyayya Aslam ya fita don kiran Mustapha Driver Ammie.

Khaleed ne kwance baisan inda kansa yake ba a gadon Asibiti.

GIDAN ALHAJI RAUF.

Sallama Akayi gidansu Lateef.

A ah ah ah bismillah Sarah kece yau a gidan namu?

Cikin murmushi takaraso.

Wata farar yarinya ce doguwa Mai Tsananin kyau daga gani 'yar gidan masu kudi ce.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now