RAYUWA TA PART 4 PAGE 5

6 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL📔📖*

'''PART FOUR 4️⃣'''

*🅿️AGE   5️⃣*

'''GIDAN HAJIA AMMIE.

Zaune kowa yake inda suke cikin farin cikin dawowar Lateef din.

Ammie ce tace saika dinga kulawa, tinda yanxu kasan makiyinka.

Ammie bantaba tinanin cewar Wannan abin zaidawo haka ba.

Sama da shekara daya sannan duk abinda ya faru bincike ne yayi bani ba.

Lateef ya fadi.

Kaga Abdul shikenan yanzu katashi muje gida kayi wanka kahuta.

Thomm!!! Daddy, Amman Salman Fa?

Allah sarki Yana Prison Amman Hankalinsa nakan Abokinsa.

Ammie ce tace Salman yana tareda Aslam basa gari.

Amman yau ko gobe zasu dawo inshaAllah.

Yanzu kaje ka huta kajiko,

Thomm Ammie.

Kallan Nadia kawai Yakeyi Lateef din,
Domin yayi matukar kewarta itama kuma haka.

Khaleed kuwa Yana Tsaye, baice komai ba.

GIDAN ALHAJI ABDULLAH.

Mahaifiyar Aslam ce zaune ita kadai tana kallan talabijin.

Mahaifin Aslam dinne ya shigo gidan bayan yin sallamar sa.

Amsa masa tayi da fadin ko kayi mantuwa ne?

No! Ba mantuwa nayi ba, Samun waje yayi ya zauna.

Dama yanzu daga wajen Mahaifin yarinyar nan nake Suhailat.

Yace yanason Ganina kuma Munyi magana dashi.

Akan auren Aslam da Suhailat din.

Tonidai kai tsaye ban tsayar masa da magana daya ba domin Ammie hankalinta yanzu ya dawo.

Kuma tacemin bikinnan tare za'ayi dana su Lateef.

Kinga kuma yanzu Lateef ya dawo bai kamata muje mata da maganar wani biki ba.

Hakane Gaskia!

Nace dashi muna bukatar wani lokacin dai Munyi magana da Aslam dinma yanzu kafin na shigo suna hanya.

To Allah ya dawo dasu lafia Cewar Mahaifiyar sa.

GIDAN ALHAJI RAUF.

Sarah ce ta shigo bayan yin sallama,

Cikin Fara'a Mama Tace Saratu kece sannu da zuwa shigo dan Allah.

Sarah murmushi tayi tace nice Mama, takarasa.

Durkusawa tayi ta gaisheda Mama,
Yanzu muke waya da Elham ai take fadamin Ya Lateef ya dawo.

Shine nace bari nazo nayi masa jaje,

Allah sarki Saratu Mungode kuwa sosai da sosai yagama cin Abinchi ma ya hau sama zaiyi wanka.

Allah ya kiyaye Gaba fadin Sarah.

Ameen ameen kawai Mama Take cewa.

GIDAN ALHAJI MUMIN.

Khaleed ne shida Mahaifin sa, da mahaifiyar sa a parlourn gidan su.

Daddy tinda Lateef din ya dawo ni ina ganin kawai kajema da Ammie maganar auren namu nida Nadia.

Wani irin kallo Alhaji Mumin yayi masa da cewa Kanada hankali kuwa?

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now