RAYUWA TA PART 6 PAGE 2

9 0 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL* 📔📖
          _( My Life )_

'''PART SIX'''

*PAGE  2️⃣*

'''GIDAN HAJIA AMMIE.

Bayan Aslam ya Huta Dpo ne Yazo Domin Jin tabakinsa dangane da Case dinsa da Murtala Mora da haryakeson Ganin Bayansa.

Dpo ne Tareda Aslam da sauran Iyalan Hajia Ammie.

Aslam Wannan Shine dalilin dayasa muke bukatar bayanai daga gareka.

Kasani haryanzu Murtala Mora Baishigo hannu ba.

Zaicigaba da farautar kane idan har baka bamu wata gaba da zamuyi amfani da ita wajen dakatar dashi ba.

Amman Dpo Narigada na dawo, Komai ya wuce...cewar Aslam.

Haryanzu Kananan da wautarka Aslam, Ammie ta fada.

Kaga Kasanar da Dpo Duk abinda kasani Kajiko.

Shine zasuyi Amfani da hakan wajen kawo karshen wannan Hayaniyar.

Shiru Aslam Yayi dajan dogon Numfashi.

Inda zai fara basu labarin Abinda ya faru a baya dalilin dayasa Murtala Mora yakeson kasheshi.

SHEKARU UKU BAYA.

Aslam ne Ya fito daga Cikin Airport  yana kalle kalle.

Abokinsa ya gano Mai Suna Tahir I Bako.

Mutuminah nazata da wasa kakemin bazaka zoba?

Haba Tahiru Tinda nace zanzo ai zanzo.

To Amman dai baka sanarwa da kowa kashigo kasar nan ba ko?

Tahiru bansanarwa da kowa ba, domin duka family na sundauka ina Cen Karatu kasar England.
To 'yan uwanka fa? Su Lateef, Khaleed?

Karabu dasu kowa a cikinsu ai yana tafiye tafiyensa ba'a iya England yake zama ba.

Yanzu haka dana tawo Lateef dinba baya kasar yana Germany kaga kuwa tinda bansa masa ido ba shima bazaisamin ba.

Sukuma sauren Sainaso muke haduwa tinda ba Apartment dinmu daya ba.

Su a tinaninsu ma Ina England haryanzu.

Hhhhh Lallai Kuwa England,
Tahir yayi Dariya.

Hmmm Kaga Yanzu Mene Dalilin zuwana Wane Mission Zamuyi?

Aslam ka kwantar da hankalin ka, Yanzu muje Hotel dinda na tanadar Mana.

Aslam bude mota yayi ya shiga yasaka kayansa a booth.

Ai Aslam Nikaina Mahaifina baisan Nadawo ba, Saina Gama Sharholiya ta tukunna zan ce masa zan dawo.

Ai kaidai bari Tahiru, Gaba daya Sai a hankali Dole musha iska ai yanzu kokuwa?

Kara Sawa sukayi Izuwa Hotel dinda zasu sauka.

Wani Tamfatsetsen Hotel ne, Iya Masu Mazajen kudine ke iya kama su domin Dakunan su daga Million ne zuwa sama.

Packing Tahiru yayi suka fito shida Aslam,

Lifter suka Shiga, izuwa dakin.

Sunata Magana, Kati Tahiru ya fito dashi.

Ya bude dakin, Wani Hayakine yake tashi a dakin na shisha.

Mata ne a ciki guda Hudu, 'yan Mata.

Sunata shaye shayen su na Magani da kuma Shisha.

Wata tana gefe tana bacchi Half naked, Wata Tana kwance Tanashan Shisha,  Watama Tanashan magani abinta.

A ah Mutumin Daya daga cikinsu ce tace lallai Oga Aslam da fadin Kadawo kenan?

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now