RAYUWA TA PART 6 PAGE 13

15 0 0
                                    

RAYUWA TA THE NOVEL* 📔📖
          _( My Life )_

'''PART SIX'''

*PAGE  1️⃣3️⃣*

_MORA BARRACK.

Jikin Aslam da Jini a galabaice yake, Suka rikoshi izuwa babbar fadar Mora dake cikin wani gari a boye inda babu kowa.

Mora ne ya fito sanye da Harami a wuyansa Dago fuskar Aslam yayi yace kagama guje gujen barin Kasar taka?

kagama duka wani guje gujenka Dama na fada maka saina kasheka da hannuna.

Saina daukarwa kanwata fansar abinda kukayi mata kaida wancen tsinannan.

Ku 'ya'yan masu kudi wato doka bata aiki a kanku ko.

Toni zan dauki hukunci akanka, Kamar yadda na kashe Tahir, Kaima yanzu zan kasheka babu bata lokaci.

Kasani babu wanda zaizo nan don cetanka domin irinku masu fyade baku cancanchi zama a wannan duniyar ba.

Mora Wata Wuka ya dauko mai Kyau sabuwa mai kaifin gaske.

Rike rigar Aslam yayi ya yanka ta sannan ya dorata akan kirjin Aslam din.
Yace.

Dama wa kaikadai na tanadi wannan sabuwar wukar tawa kai Marar Mutunci.

Yanzu zaka zama tarihi.

Saman Katanga Khaleed ya duro a tsakiyar inda suke.

Mora Kallan sa yayi da cewa waye kai?

Nidan Uwan Sane, Karabu dashi bayada laifin komai fadin Khaleed.

Bayada laifin komai fa kace?
Su kama kanwar tawa suzomin da magana da soyayya susa na yarda dasu na amince dasu.

Sannan suci Amanata suyi mata fyade yanzu ka fadamin wai baisan komai ba?

Nasan duka Abinda ya faru kuma ina mai baka hakuri abisa mutuwar kanwarka.

Amman kamar yadda na fada maka kana bukatar bayani Malam Murtala.

Kasani kaifa ba makashi bane Malami ne, kuma kasan hukuncin duk wanda ya kashe wani.

Kada kayi kokarin daureni da wannan surutan banzan naka, A baya ne nake malami yanzu niba malami bane.

Sannan kasani niba makashi bane, Barna nake gyarawa domin gwamnati batayi komai akansu ba da suka kashemin kanwata.

Kayi hakuri nayi maka Alqawarin zaka sami Adalchi amman da fari ka saurareni kada ka cutar da Aslam.

Murtala Mora Idonsa jajawur yayi, da cewa karigada ka makaro, Wukar ya dabama Aslam a cikinsa.

Aslam wata kara yayi, Khaleed din matsowa zaiyi murtala Mora yace kana dada wani takun zanyanka wuyansa a gabanka.

Kasan babu hadina dashi kumazan iya.

Kasaurareni Murtala, Wannan abinda kakeyi kuskurene kasani doka zatayi aiki a kanka.

Dokar Banza da Wofi, Dokar da takasa daukan mataki akan wanda suka mashe marainiya.

Suka jefar da ita, ko tausayi babu Kafadamin wannan wane irin rashin imani ne haka?

Yaran Mora ne A cikin filin wajen suka Tsaya.

Mora wuka yasa zai yanka wuyan Aslam,

Khaleed ne ya ciro wayarsa yajefa inda ta daki hannun Mora wukar ta fadi.

Cikin haushi Mora yace kayi kuskuren zuwa wannan wajen, Kasaka Kanka cikin rigimar da babu ruwanka.

Kasani yanzu zankasheka anan sannan shima nakasheshi Anan.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now