*RAYUWA TA THE NOVEL*✍🏽📔
_Page 6_
'''Saukowa Sukayi Kasa wasu samari suka kara Tambaya.
Dan Allah Biro muke tambaya?
Kinga Biro gashi cen zaishiga Mota, Kuje fita zaiyi daga Makarantar.
Mungode Wata Tsinanniyar Motace Ya bude ya shiga Wayarsa ya dauka Mai tsananin tsada wadda ake yayi ta zamani
Irin kuma wadda Lateef ya siyawa Nadia itace a hannunsa, iPhone 14promax. Thom Mama zanzo yanzu inshaAllah.
Sannu, Sauke gilashin Motarsa yayi da cewa Yauwa sannunku.
Dan Allah wajenka mukazo,
Amm! Kuyi hakuri yanzu zandan fita ne.Amman idanna dawo kusameni a Library kunji Biro ya fada musu haka.
Juya motarsa yayi ya wuce ya barsu, Kai Aysha Wannan Biro din bashida Mutunchi gaskia.
Hmmm Wallahi Yanada Mutunchi dandai mu matane yasa yayi mana haka.
Kamaryaya dan mu matane naga muma yafi kamata ya bukata don taimakawa ai kokuwa.
A ah shikam dai ba haka yake ba shi babu ruwansa da mata duk kyaunki baki isa biro yace kinma burgeshi ba ballan tana yace yana sonki.
Akwai abinda ban fada muku ba akansa, Mahaifin Biro yana daya daga cikin masu kudin wannan garin ko kuma ma ince Ahalin su baki daya.
Idan kinga yadda mata suke rububinsa wallahi sai abin yabaki mamaki Nusaiba.
Saboda biro kobadan soyayya ba kaso Alaqa dashi don kokarin sa.
Gashi kuma kyakkyawa Fari,
To Aysha ko kema kina Sonsane?
Nusaiba wallahi da ace banida wanda zan aura tabbas biro ya kai namijin da zanso na samu.Babu abinda ya rasa Ga Ilimi, kyau Kudi Hankali komai ya hada.
Kunga muje muyi Sallah Da Allah Fadar Nadia.
Shin wai kunyi waya da Lateef kuwa? Nusaiba ta tambayi Nadia.
Wallahi Inata nemansa Amman wayarsa bata shiga idanna koma gida zan kira Salman ko yanada wata Number shi mai shiga.
Ok! Muje dai muyi sallah saimuci abinchi.
GIDAN ALHAJI MUMIN.
Mama ce itada Suhailat a Parlour sunata hirar su.
Sallama Akayi Ba kowane ya shigo ba, sai Aslam.
A ah Yaudai ga Mutumin a gidana fadar Mama.
Murmushi kawai yayi yace Mama Ina wuni?
Lafia qalau Aslam ya Maman naka da kuma Daddyn ka?Wallahi duk suna Lafia lau,
Toh Masha Allah, Zauna Mana.Suhailat tana Zaune Ko kulashi batayi ba Alamu sungwada Haushinsa ma takeji.
Yaushe kikazo Nan Suhailat Aslam ya tambayeta.
Kallansa kawai tayi Tace Jiya,
Mama Kince kinason Ganina Makaranta na baro nazo.
Khaleed ne yashigo dacewa murya nakeji Kamar ta BIRO!!! cikin tsokana.
Mtsww Kai wai banace kadaina fadamin sunan nan bane? Aslam yace.
BIRO!!! cikin tsokana Khaleed ya kara fadi.
Haba Malam Biro ya haka kuma nifa Abokin kane?
Kaii kaii! Khaleed bakajin magana ko mene Wani Biro?
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
Ficção GeralLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?