RAYUWA TA PART 5 PAGE 7

9 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖

'''PART FIVE (5)'''

*PAGE SEVEN (7)*

'''GIDAN SU SARAH.

Radeeyah ce zaune itada Aunty Nafi.

Sarah ce ta fito sanye da doguwar rigarta me kyau.

Da makullin motarta a hannu.

Aunty zanje Shopping daga nan kuma zan wuni gidan Ammie.

Banje nayi musu jajen Batan Aslam ba Kuma Lateef ya sanar dani tin kafin ya tafi.

A ah, To ai da kin sanar dani sa wuri da kawai munje gaba daya kafin Alhaji ya fita na tambayeshi.

Babu damuwa kwaje ko gobene Babu matsala Mansur ya kaiku.

Radeeyah ko kula Sarah batayi ba hankalinta nakan wayar ta.

Tanata murmushi abinta.

Keee!!! Anata magana kinyi shiru bakice komai ba Aunty ce tafadi wa Radeeyah.

Hmmm Aunty kenan, ai haka take Jiyama Ni hanani bacchi tayi tanata waya da Saurayi.

Har kusan 3 na dare.

Radeeyah dawa kike waya karfe uku na dare?

Aunty Kinsan dai lokacin nan da Germany ba iri daya bane.

Ina magana ne da wanda zan aura da yake cen.

Kuma kinga dole shine lokacin daya dace.

Aunty cewa tayi Allah ya kyauta.

Sarah fitarta tayi Abinta.

GIDAN HUTAWA NA HON. ABU.

Ka kwantar da hankalinka, Shi wannan zargi ne kawai.

Amman zaka iya fada mana Alaqar ka da ita matar Aslam din?

Dpo ya Tambayi Abu Adam.

Amm Dpo Ita Kanwata ce,

Kanwarka kokuma 'yar uwarka?

'Yar uwa ta, Dpo.

Tokuma kace mana kanwa kuma munsan dai babu aure tsakaninka da kanwarka.

Kuma anbamu statement akan cewar kana sonta kuma kaso auren tama.

Allah ne baiyi ba.

Ehh hakane, Tabbas nasota.

Kafin tayi aure, Kuma da tayi aure saina fahimci cewar dama ba rabona bace itadin kawai Na hakura

Ok, Amman meyasa ka hakura Honourable?

Dpo yanzu kace Allah ne baiyi na aureta ba.
Saboda haka Allah ne baiyi ba.

Ok Naganeh, Toshikuma Aslam dinfa Mecece Alaqar ka dashi?

Hmmm Dpo wannan wace iriyar tambaya ce kuma?

Tambaya ce Honourable amsa kawai zaka bayar ai.

Ok, toni banida wata Alaqa dashi,

To amman baka ganin tinda yana auren 'yar uwarka, Ko ince kanwar kama.

Shiba sirikinka bane?

Kodai Kana Kishine?

Abu Adam shiru yayi Inda Ya dauki Ruwa a Glass Cup yasha.

Amm! Dpo Banida wata Alaqa dashi.

Kuma Dashi da itadin duka A halin yanzu ba ruwana dasu idan kundauki hakan a matsayin donna rasata ne toshikenan.

But Gaskia, Nagaji da Amsa irin wannan tambayoyin naka Dpo.

Hmmm Honourable kenan, Kasancewar nine akan case din nan shiyasa banbari kowane yarona yazo domin questioning dinka ba.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now