*RAYUWA TA THE NOVEL* 📔📖
_( My Life )_'''PART SIX'''
*PAGE 9️⃣*
'''GIDAN SU SUHAILAT.
Mahaifinki ya gaji da ganinki a haka Saboda haka nafita donna sanar dake abinda yace na sanar dake.
Ki kuma dauki wayanki kiki rashi Kiji daga bakinsa.
Cewar Aunty Fateemah Mahaifiyar Suhailat din.
Suhailat tsaye take takasa cewa Komai a zuciyarta tace Amman Daddy yasani cewar da Aslam kadai zan iya rayuwa ta.
Meyasa zaimin haka?
Sama tahau izuwa dakinta batace komai ba ranta a bace yake.
DA DADDARE.
Khaleed ne Cikin wata unguwa ta masu kudi.
Wayarsa ya dauka Yayi kira, Hello Gani Nazo.
"Ok Kashigo Toh, Ina Nan Garage"
Muryar Macece a wayar.
Khaleed fitowa yayi sanye da wani Yadi a jikinsa, Yayi kyau sosai sai kamshi yakeyi.
Shishi kadaine Abinsa.
Knocking yayi megadi ne yace Yess Wane?
Budewa Yayi Sannan Yace Allah ya taimakeka, Me Gida Khaleed!
Khaleed Mamaki Yayi domin dai yasan me gadin baisanshi ba tayaya yasan sunansa.
Amman Ya Akayi kasan sunana?
Ai Karamar Hajia ta sanar dani cewar zatayi bako kuma yana hanya sunan sa Khaleed idan kazo kashiga.
Ok! Khaleed ya fada, Toya kake ya aikin?
Lafia Lau Alhmdullh Me gida Khaleed,
Kaga Mene Sunanka?
Ni sunana Kamalu,
Toh Kamalu Ni kuma sunana Khaleed ne ba Megida Khaleed ba.
Kakirani da Hakan Babu damuwa Kaji.
A ah Me Gida Khaleed ai bazan iyaba duk abinda Karamar Hajia tace natane.
To dole mu girmama wannan abin, Saboda haka Me Gida Khaleed bazan iya fadin sunanka kai tsaye ba kaga farceni.
Khaleed cewa yayi Allah Ya kyauta Cikin Murmushi.
Karasawa yayi, Wata Doguwar Yarinya ya gani daidai daidai, Itaba Bakaba Itaba fara ba.
Abindai gashinan Sanye take da wata zukekiyar Abaya a jikinta.
Da kuma wayarta me Asalin Tsada Kirar iPhone ta Zamani ta yayi.
Murmushi Tayima Khaleed din, Karasawa yayi.
Dan Durkusawa tayi ta gaisheshi Barkanka da zuwa Yallabai.
Khaleed Murmushi kawai yayi mata dacewa yallabai kuma sunan da kika bani kenan?
Cikin Fara'a Tace Ehh Ai sunanka babban Suna ne nima yayimin girma na fadeshi kai tsaye.
Khaleed kam yaji dadin hakan, Har zuciyarsa yasan cewar yanzu ya sami macen aure.
Tabbas wannan Tayi Daddy, Kuma Tabbas Ina Kaunarta Cewar Khaleed a zuciyarsa.
Mushiga Babban Parlour, Abban Mu Yana ciki dama yasan da zuwan ka saiku gaisa.
Khaleed cikin yanayi na nutsuwa yace thom Ai babu damuwa.
Jiddah shigewa gaba tayi Khaleed na biye da ita a baya.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
General FictionLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?