RAYUWA TA PRT 2 PAGE 13

9 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*✍🏽📔

✨ _PART  2_  ✨

1️⃣3️⃣

'''GIDAN ALHAJI ABDULLAHI.

Nadia ce zaune kusa da Maman Aslam.

Toh Amman Nadia ya kika tawo keke kadai idan da wani abu ya sameki fa?

Mahaifiyar Aslam ce ta fadi haka.

A ah Mama nasan cewar babu abinda zai sameni domin nagane hanya.

Mama na kasa yadda cewar wadancen sune 'yan uwana domin.

Saboda Basaso na auri Aslam,
Wani sukeso su auramin daban.

Kinga kiyi shiru Kinji karki damu yanzu Alhaji zai fito saimuga abinda za'ayi.

SOMEWHERE IN THE STATE.

Aslam ne cikin motarsa shida Suhailat.
Fuskar Suhailat cike take da damuwa.

Aslam tinda na fada maka abinda Daddy na yace akan aurenka kaki kace komai.

Aslam ne yayi mamakin yadda mahaifin Suhailat bai sanar da ita cewar Aslam dinne baya sonta ba.

A zuciyarsa yace Kenan Mahaifin Suhailat ya rufa mata ne don kada wani abu ya sami 'yarsa?

Suhailat Kiyi hakuri!

Daddyn ki yanada uzirinsa na fadin hakan wanda ke baki sani ba.

Amman Aslam Daddy bai taba hanani wani abuda nakeso ba.

A koda yaushe burinsa na sami abinda nakeso amman yanzu na kasa fahimtar sa.

Aslam ne yace Suhailat zaki fahimta domin Daddy bazai hanaki abinda kikeso ba haka kawai?

Kiran waya ne ya shigo masa inda ya daga da cewa.

Hello Ammie...

"Kazo yanzu yanzu inason ganinka gidana"

Thomm Ammie ganinan fadin Aslam.

Meyafaru?

Ammie ce tace tanason ganina,
Thom muje mana..

Shikenan inji Aslam.

GIDAN ALHAJI ABDULLAH.

Nadia ki kwantar da hankalinki,
Babu wanda zaiyi miki auren dole kinjiko.

Suma basu fahimceki bane amman karki damu.

Duk halin da ake ciki bazan bari ki auri wanda bakyada ra'ayinsa ba.

Nadia kawai girgida kanta tayi tareda cewa Nagode sosai daddy.

Fito da wayarsa yayi daga Aljihunsa inda yace hello Ammie.

"Kazo gidana Abdullahi Yanzu yanzu"

Cikin biyayya yace thom Ammie ganinan zuwa..

"Kuma kazo tareda Nadia"

Yayi mamakin yadda akayi Ammie tasan Nadia tana gidansa.

Cewa kawai yayi thom Ammie babu damuwa.

Meyafaru Alhaji?

Ammie ce tace naje yanzu kuma tareda Nadia.

Amman ya akayi tasan Nadia tananan?

Nima banida Amsar wannan tambayar...

Jeki shirya kufito muje.

GIDAN SU NADIA.

Indai har kunason kasancewa na a raye to lallai ku nemomin Nadia.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now