*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖
'''🅿️ART 3️⃣'''
*PAGE 7️⃣*
''' GIDAN HAJIA AMMIE.
Lateef ne zaune shida Ammie,
bude kofa Akayi Inda Nadia ta shigo itada Aslam.
Lateef tashi yayi yace Shikenan Ammie nizan tafi..
A ah yaya muna cikin magana ka tashi kace zaka tafi?
Ammie kawai zandawo daga baya,
Dan Allah ka tsaya Lateef cewar Nadia cikin sassanyar murya.
Kallan fuskarta yayi yace Na tsaya?
Tona tsaya nayi miki me, Kona tsaya ki kara rainamin hankali kamar yadda kika saba Nadia.
Kinga Lokaci yayi da duka zamu daina yaudarar kanmu batani kikeba.
Izuwa yanzu kinmun abubuwan da ya kamata na gane amman bangane ba.
Idan a baya bakida lafia yanzu fa?
Nadia bazan iya jurar ina sonki kuma kina tarayya da wani ba koda Dan uwana ne this is the fact.
Kije ki rayu dashi ki auri wanda ya dace nima zanje na nemi wadda ta dace.
Lateef sauri yazo zai fita Aslam tsayawa yayi a gaban sa.
Yaza kace haka Abdul Lateef?
Kanaso kace macece zata rabani da kai?Hmm shikenan, Haryanzu Nadia bata fadamin cewar bata sona ba wannan shine dalilina naci gaba da bibiyar ta.
Aslam kallan Nadia yayi sannan yace Nine na shigo rayuwar ku daga baya Saboda haka ba kaine ya kamata ka rabu da ita ba nine....
Nadia kiyi hakuri, Anan ne muka kawo karshen wannan Alaqa nidake saboda Dan uwana Ya rigani Ke.
Bazanso kaina na cigaba da tarayya dake ba Kiyi hakuri!
Kaiii! Wai mekuke nufi ne dukan ku meyake faruwa?
Babu komai Ammie basai kinji me yake faruwa ba.
Amman Yanzu dai ya kamata kisani cewar Nadia Lateef ne wanda takeso.
Nadia kallan Aslam din tayi cikin wani irin kallo idonta yayi jaaaa.
Allah ya kaddara Saduwar mu..
Aslam fita yayi daga cikin Parlourn yayi tafiar sa.Lateef da yake tsaye ne ya kalli Nadia.
Itama kallan sa kawai tayi.
DA DADDARE.
Aslam ne yafito daga cikin Mota ya shiga gidan su Suhailat.
Knocking door din yayi, Suhailat ce tazo ta bude.
Shigo...
Aslam tsaye yake Suhailat cewa ta karayi Kashigo Mana.
Tinanin me kakeyi?
Hmm Babu komai Aslam shiga yayi inda Suka Gaisa da Aunty Fateemah.
Alhaji yana Parlourn sa dama yace zakazo kashiga koh,
Thomm Aunty cewar Aslam.
Assalamu Alaikum.
Wa'alaikumu Assalam Aslam harka karaso?
Ehh Daddy harna karaso ina wuni?
Lafia lau Aslam yakake ya Office?
Lafia Alhmdullh Daddy.
Tho Masha Allah.
Ahh Aslam nasan kasan dalilin dayasa nace Kazo?
Ka kumasan akan abinda zanyi maka magana.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
General FictionLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?