RAYUWA TA PRT 3 PG 10

17 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖

'''🅿️ART 3️⃣'''

*PAGE 🔟*

'''Me kikeyi Anan?
Lateef ne ya tambayi Nadia.

Ehm Dama, Munzo ne

Wai Nadia meyake damun kine?
Meyasa bakyamin Adalchi?

Jimana Lateef ya kake Mata Fada ne wai?

Dan ta fita dani shine tayi maka rashin Adalchi?
Kai waye a wajenta da yasa tayi maka rashin Adalchi?

Sannan ma Kai batace kayi mata rashin Adalchi ba sai kaine zaka fadi haka?

Banyi Magana da kaiba Khaleed, karka samin baki cikin magana.

Tinda kake magana da Wadda zan aura ya zama dole na taka maka birki tinda ba tsoronka nakeyi ba.

Cewar Khaleed.

Ba yaudarar ta kakeyi ba idan ba haka ba kaima ubanme kazoyi nan kaida Sarah?

Ko kazata bansan komai bane?

Nadia wani irin kallo Tayima Lateef din Nan da nan idonta yayi jaaaa...

Sarah kallan Nadia tayi a zuciyarta tace Ok! Wannan ce Nadia kenan...

Kinga Nadia wuce muje da Allah Khaleed yaceda Nadia.

Lateef ya kasa cewa komai harya fara fada kuma shima bashida Gaskia.

Nadia! Nadia!! Lateef yake kiran sunanta Amman tayi banza dashi Tabi Khaleed din sukawuce.

Wannan ce Nadia wai? Sarah ta tambayi Lateef.

Shiru kawai yayi mata.

Bude Mata Kofa Khaleed yayi tashiga Motar sa.

A zafafe ya taka motar suka tafi,

Karka maidani gidan Ammie ka kaini Gida kawai Nadia taceda Khaleed.

Meyasa Nadia?

Khaleed kawai ka kaini gida,
Banason Komawa cen din.

Shikenan, Amman kiyi hakuri nasan ranki ya baci.

Nadia Banaso ranki ya dinga baci akan karamin abu haka.

Khaleed wannan ne karamin Abu?
A hakan sona yakeyi Kuma yana so na aureshi amman yaudara ta shigo cikin lamarin.

Bazan iya Ba Khaleed, Nima zan zabama kaina Abinda yafi dacewa dani kawai.

Kinga kada kiyi saurin fushi nima dana fadi hakan na fadane saboda yayi miki fada raina ya baci.

Amman magana ta gaskia bansan Alaqar sada Sarah ba.

Amman a baya dai budurwar sace Kowa kuma yasan sun rabu.

Bansan me sukeyi a nan ba bazanyi masa sharri ba gaskia.

Khaleed koma mene Dai ai gashi na gani da idona.

Na rabu da Aslam saboda shi naki baka fuska duka saboda shi.

Amman shi yanzu da abinda zai sakamin kenan.

Shikenan ya isa Nadia kidena fadin haka kishare hawayenki Yanzu ina nan ai tare dake.

Bazan barki ba kinji koh?

GIDAN SU NADIA.

Assalamu Alaikum.

Oyoyo Yaya Nooratu sannu da dawowa.

Kindawo lafia Ya Cen inda kika baro Nusaiba take fadi.

Sassannunku dai Umma Ina wuni Nusaiba yakuke?

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now