tRAYUWA TA PART 5 PAGE 6

10 0 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖

'''PART FIVE (5)'''

*PAGE SIX (6)*

'''GIDAN ALHAJI MUMIN.

Saukar Mari kakeji Tassss a fuskar Khaleed inda mahaifinsa ya mareshi.

Haba Alhaji Mahaifiyar Khaleed ta fadi cike da Tausayin Khaleed din.

A gefe Nadia ce tsaye.

Kibarni dashi, Soyake Ya doramin hawan jini.

In banda shashanci da rashin hankali ace ya baro kasar dana turashi batare da sanin kowa ba.

Idan wani abu ya sameshi fa?

Duk ina tinanin na turashi cen don hankalin sa da namu ya kwanta amman shi gaba daya baya ganin wannan.

Alhaji Mumin ne yake fadin haka,

Alhaji kayi hakuri kasan yaro ne,
Duk kece kike daure masa gindi daga anyi abu kice yarone.

Da yarintar da rashin hankalin yakeso na aurar dashi.

Toh kasani Abinda kayimin a baya na dauka wallahi this time around bazan dauka ba.

Khaleed you ve to come back to your senses!

Am tired of nonsensity and stupidity!

Sannan Ina kaje kakai Aslam?

Cikin Yanayi na Mamaki Khaleed din ya kalli mahaifinsa.

Daddy Bayaga fada da kayimin Akan Komai kuma har kana ganin zan iya dauke mutum?

Mutum dinma Dan uwana?

Kaga Wannan Shaukin Naka, kabari kayishi daga baya kasanar dani inda Aslam yake idan ba sokake

Idan Ranka yayi dubu saina batashi ba.

Daddy Wallahi da gaske nake, Bansan Komai ba.

Banida wata masaniya Akan Inda Aslam yake.

Banmasan cewar bayanan ba,

Daddy Tabbas Inason Nadia Kasani Daddy.

Amman Sonda nakeyi Mata baikai na iya sace Mutum harna boyeshi ba.

Kayarda dani Daddy.

Mahaifin Khaleed matsowa yayi kusa dashi,

Kasani Idan Wani Abuya sameshi bazan taba yafe maka ba Khaleed.

You've to be very very careful kuma idan ka manta zan tina maka.

Nadia matar aure ce, Cigaba da bibiyarta Bacin rai kawai zai cigaba da kawo maka.

Mahaifin Khaleed din wucewa yayi izuwa dakin sa.

Nadia tsaye take batace komai ba.

Saida safe Mama, Ta fadi jikinta a sanyaye.

Mahaifiyar Khaleed din ce mata tayi saida safe Nadia.

Wajen Khaleed din tazo inda tace meyasa bakajin Magana ne Khaleed?

Amman Mama yaudarata fa Akayi,
Aka turani Wata kasa don Nadia tayi aure.

Khaleed mahaifin nakane ya yaudareka?

Waishin yaushene zaka nutsu khaleed?

Kasani duk wannan abin da mahaifinka yakeyi yanayi ne saboda farin cikin ka.

Kasani wannan shine hanyar da kadai zai saka farin ciki amman kai baka gani.

Yakamata ace kasani yanzu Nadia tayi aure.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now