RAYUWA TA PART 6 PAGE 5

15 0 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL* 📔📖
          _( My Life )_

'''PART SIX'''

*PAGE  5️⃣*

'''KOFAR GIDAN SU NUSAIBA.

Nusaiba Cikin Wani irin Kallo ta kalli Oga Muhktar,

Gida zata shige, Kiran sunanta yayi da cewa Nusaiba wajenki nazo fa.

Dan Allah Dan Annabi katafi, Wannan Shine wanda zai aureni Shin Munyi masa adalchi a gabansa kazo wajena?

Ehmm, Nusaiba kitsaya kiji dame yazo ki saurareshi, Ni na wuce saida Safe Allah ya tashemu Lafia.

Oga Muhktar din ko Salman dinma bai kulaba.

Dan Allah Oga Muhktar kayi hakuri, Kai Musulmi ne nasan kasan haramunne nema kan nema.

Kuma na tabbata kasan hukuncin?

Nusaiba Ehh Nasani, Amman kisani bannemeki Akan neman wani ba.

Ni ni kadai nasan ina sonki, Kuma fiye da kowa.

Meyasa kikeson Nunamin cewar akwai wanda yake sonki bayanni ne wai?

Oga Muhktar Akwai Kuma Gashi ka ganshi, Shine wanda Zai aureni.

Ya kawo kudina, Kuma Lokaci kawai muke jira.

Amman Nusaiba meyasa kikamin haka?

Meyasa zaki cutar da zuciyata?

Bayan kinsan cewar kekadaice wadda nakeso?

Oga Muhktar, Nice wadda ka cutar don't try to blame me, Nabaka dukkanim wata dama.

And at last you ruined it.

Banida Option daya rage naso wanda yake sona.

Dan Allah Don Girman Allah kafin hakurin Bawan Allah nan ya kare takaiga harya fara mayar da martani kadaina bibiyar matar da zai aura.

Wannan Taimakon Nakeso kayimin.

Kasani saboda hakane yasa ya hanani zuwa aiki yanzu saboda bayaso wani yayimin maganar wani.

Dan Allah Oga Muhktar Kayi hakuri ka dauki Kaddara Kamar yadda tazo Mana duka.

Nusaiba shin Kina Sona kobakya sona?

Oga Muhktar Yanzu Magana Akeyi ta zanyi aure, Shin idan banason mijin da zan aura zan aureshi ne?

Idan kuma har ina sonsa mezaisa naso wani?

Banason kifadamin Abinda zaki sani tinani akai kawai kifadamin Answer na straightforward.

Oga Muhktar Inason wanda zan aura indai kuma Ina sonsa ya tabbata Banason kowa bayan shi.

Ok! Tohh Haka zakicemin, Yanzu nagane kuma nasan dalili.

Babu damuwa inshaAllah  Nusaiba Bazan kara zuwa wajenki ba.

Nima daga yau zanje nayi RAYUWA Ta.

Cikin fushi Oga Muhktar Ya nufi Motarsa.

Nusaiba tsaye take Domin Oga Muhktar yana shigar mata kaida yawa.

WASHE GARI.

Khaleed ne Shida Suhailat a Garden na Gidansu Suhailat din.

Suhailat A halin Yanzu we have no choice, Ya Kamata ko kuma ince lokaci yayi da muma zamu fuskanchi gaban mu.

Musan inda muka nufa,

Khaleed mekakeson cewa?

Suhailat A daren jiya Na dade Maganar Mommy tana dawomin a kokon kaina.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now