RAYUWA TA PART 6 PAGE 12

15 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL* 📔📖
          _( My Life )_

'''PART SIX'''

*PAGE  1️⃣2️⃣*

KOTU.

Suhailat ce tashiga Akwati Donjin wace hujja take dauke da ita a kotu.

Lawyern wanda suke karane Ya karasa donyima suhailat tambayoyi.

Malama Suhailat shin zaki iya fada mana mene Alaqarki da Honourable Abubakar Adamu?

Banada wata Alaqa dashi,

To Amman kuma A yadda bayanai sukazoma kotu shine Kuna aiki tare dashi don ganin kuncinma burikanku duka, Shin me zaki iya cewa zangane da hakan?

Banada wani buri daya wuce nida Ahalina muzauna lafia.

Nafahimchi hakan bazai taba yiwuwa ba har sai na matsar da babban matsalar da take cikin familyn mu wato Abubakar Adamu.

Hakan yasa nashiga jikinsa da niyar zamuyi aiki tare dashi donya sami biyan bukatarsa nima kuma haka.

Wanda a zahirance shi yanason raba Dan uwana Aslam da Matar sa Nadia.

Nikuma na dau Alwashin bazan taba bari hakan ya faru ba.

Hakan yasa a duka gidan na dasa na'urar nadar murya wanda duk abinda aka fadi a cikin gidan zanjishi.

Abubakar Adamu yarasa meyake masa dadi ashe dama yarinyar nan zuwa tayi ta yaudareni?

Yaso kawarda ita saidai tafishi xafin naman aikata hakan.

Abinda yaketa fadi kenan a zuciyarsa.

Wannan shine kawai abinda nasani cewar Suhailat.

Hajia Ammie Hada ido sukayi da Mahaifiyar Suhailat wato Aunty Fateemah.

Shikenan zaki iya komawa kizauna Malama Suhailat.

Lawyer ya fadi, Ya mai girma me Shariah duba da hujjoji da muka kawo gaban wannan kotu mai Albarka hakan yana nufin Honourable Abubakar Adamu Mugun mutunne.

Tinda har baiji kunyar hada kai da 'yar uwar wanda zai cutar ba.

A gefe guda kuma ya bada umarnin a rabashi da duniya baki daya sannan a batar da gawarsa.

Ina rokon Wannan kotu mai Alfarma data bima wanda yake kara haqqinsa domin yin hakan shine zai kara tabbatar da adalchin wannan kotu.

Lawyern Honourable ne ya kalli Abubakar Adamu da girgida Kansa.

Bayaga hujjoji da aka kawo gaban wannan kotu, Honourable Abubakar Adamu ya tabbata mai laifi kamar haka:

Kokarin aikata kisan kai,
Yin Zanba Cikin Aminchi,
Da kuma Tada zaune tsaye.

Wannan kotu mai Adalchi ta duba laifukan da ake zargin Honourable dasu da kuma tabbatar da laifukansa.

Kotu ta baiwa Jam'iyar da Honourable Abubakar yaje ciki umarni da ta soke takardar Takarar da yake nema ta gwamnan wannan jiha tamu mai Albarka.

Duba da wani sashi na dokar zama gwamna, sannan kotu ta yankewa Honourable Abubakar Adamu Hukuncin Shekaru Shida A Gidan Kaso tareda aikin wahala Kuma Babu beli.

Kotu ta tashi!!! Daga Bakin Alqali.

Kowa Cikin Mamaki yake domin babu wanda ya taba tinanin cewar Suhailat bata daina son Aslam ba.

Nadia ce ta rungume Suhailat din cikin kwalla da fadin Mungode sosai Suhailat.

Aslam kallan Suhailat yayi da cewa Basaina fada na gode miki ba kinsan na gode cikin yanayi na wasa.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now