*RAYUWA TA THE NOVEL✍🏽📔*
✨ _PART 2_ ✨
6️⃣
'''HOSPITAL.
Dpo ne tareda Khaleed Ammie tana zaune.
Kaga kadage ka tina sosai meyafaru da Nadia kaji?
Nifa abinda zan iya tinawa shine Nadia zata bude kofa na hanata.
Garin cire hannunta daga jikin kofa shine wannan Al'amari ya faru bayan wannan babu wani abu da zan iya tinawa.
Ok! Shikenan kasamu ka huta zamu dawo daga baya.
Hajia Zamu dawo idan ya samu ya huta haryanzu yana cikin wani yanayi ne.
Shikenan Dpo! Babu damuwa.
Kaimeya kaika zuwa ka dauki Yarinya wai zaku gudu?
Meyasa Khaleed bakajin magana ne?
Ammie nace ku auramin ita Kunki ya zanyi Ina matukar son Nadia sosai.
Ammie ina son Nadia fiye da sonda nakema kaina.
Kaga Dallah Shashasha dakata.
Kana sonnata shine zaka dauketa batareda sanin iyayenka ko nata ba kuje kuyi aure.
Wannan shashancin naka yayi yawa ai.
Yanzu toh tana ina Nadia duk a dalilin wannan shirmen naka gashi bamusan inda take ba duka.
Shiru Khaleed yayi.
Ammie wallahi idan ban auri Nadia ba mutuwa zanyi....
Kai! Kull karna karaji kayi wannan furucin,
Kuma Nadia ko dawowa tayi na Haramta maka zuwa wajenta.
Wannan shine punishment dinka.
Haba Ammie Yazakice haka?
Wallahi Ammie Nadia itace Rayuwa Ta. Kuma Inba Nadia...
Nace karka kara fadin haka ko?
Kasan mene Rayuwa kuwa da kake cewa Nadia ce rayuwarka.
Da kuma da bakasan Nadia ba fa baka rayuwa ne kome?
Kull Na fada maka Karna karaji ka fadi wannan Maganar inba so kake na sabar maka ba.
Kiyi Hakuri Ammie.
GIDAN SU NADIA.
Kiyi hakuri Umma inshaAllah za'a ga Nadia Yaya Nooratu ce ta fadi hakan.
Umma inshaAllah za'a ganta Ammie ta dora Jami'an 'yan sanda domin bincike kuma Nan bada dadewa Ba za'a sameta inshaAllah.
To Allah yasa!
Amman Ace Mahaifin yarinyar Nan ko shekara baiyi da rasuwa ba yanzu Annemi 'yarsa Anrasa.Dama Babu irin maganganun da bamu shaba akan rasuwar nan tasa itama Nadia ana cewa yanzu saurayi tabi suka gudu.
Umma duk maganganun da mutane suke fada basune abin dubawa ba.
Muyanzu ta yadda za'a sami Nadia mukeyi.
Mutane kuma dama kome akayi saisunyi magana idan zakibi gida gida kina Rabawa Mutane Abin Alkhairy a madadin wasu su gode miki.
Bincike da zargi zasuyi akan ya akayi kika ma sami wannan har kike rabarwa mutane ba'a iya musu Umma.
Fadar Nusaiba.
GIDAN ALHAJI ABDULLAHI.
Amm! Yanzu ke babu wani abuda zaki iya tinawa?
Mahaifin Aslam ne yake tambayar Nadia bayan ta farfado.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
Ficção GeralLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?