*RAYUWA TA THE NOVEL📔📖*
'''PART FOUR 4️⃣'''
*🅿️AGE 1️⃣1️⃣*
'''THE NEXT DAY.
OFISHIN NADIA.
Nadia ce zaune kan kujera a Office dinta takasa aikin komai.
Wayarta ta dauka ta kira Salman,
"Hello Nadia"Salman Banji daga gareka ba tinjiya Haryanzu Lateef baya daga wayana
"Nadia karki damu Zanje Zamuyi magana dashi bansameshi bane jiya"
"Amman yanzu inshaAllah zanje zakuma muzo tare dashi"
Thom shikenan nagode Salman,
Karki damu Nadia yima kaine.
PRIVATE HOSPITAL.
Lateef ne Yabiyo exactly inda Sarah tayi masa kwatance.
Knockin Kofar yayi Aunty Nafi ce tace shigo Mana Lateef.
Shigowa yayi ya gaisheta,
Ya Maijikin Kuma Aunty?Mai jiki gata nan Lateef jiki Da sauki Alhamdulillah.
Masha Allah, Allah ya kara sauqi.
Sarah taji dadin zuwan Lateef Sosai da sosai domin kuwa ganinsa da tayi taji duk ciwon ta ya tafi gaba daya.
Mahaifin Tane ya shigo dakin, Karaf yaga Lateef a cikin dakin.
Meyakawo ka Nan?
Shin mekazo kace ko kuma kayi?
Kace bazaka kara zuwa wajen 'yata ba yanzu meya kawoka?
Mekazo kamata?
Abbah....
Kaga bana bukatar jin komai daga gareka Mallam.
Kafita daga nan, kuma karka kara dawowa kasani bama bukatar zuwa dubiyar ka.
Koda kai ko babu kai Sarah zata sami lafia.
Amman Abbah dan Allah ka saurareni Mana...
Wallahi Tallahi sa'arka daya nan asibiti ne inbadan haka ba da baka tsaya a gaba ba Daka dade da kwanciya a kasa kana numfarfashi.
Kafice daga nan kafin na manta cewar nan asibiti ne na bigeka anan..
Abbah, Sarah ta fada cikin Sassanyar muryar ta.
Shhhhhhh!!! Karki cemin komai kema bar ganin kina gadon asibiti kimin shiru karna dawo kanki.
Aunty Nafi kuwa, tarasa abincewa.
Lateef cikin yanayi na abin tausayi ya kallo Sarah.
Kawai ya fita.
Sarah hawaye ne yake fitowa a idanuwan ta.
GIDAN SU NADIA.
Abu Adam ne ya fito daga motar sa ya shigo cikin gidan.
Su Umma ne suke masa lale, samun waje yayi kan kujera ya zauna.
Umma banga kunata shirye shiryen komai ba biki ya matso babu wani shirye shirye da kukeyi.
Ina Ita Nadian take?
Shiru sukayi dukansu.
A ah, Umma ina Magana Ina Nadia take yaya dukanku kukayi shiru kuma?
To Nadia dai yau Kusan Satinta daya Bata kwana a gidan nan.
Tin sanda ka kawo kudin nan tace babu wanda ya isa yayi mata auren dole.
Hakan yasa tabar gidan, akwai Limamin Unguwan nan,shine wakilin Nadia kaje ka sameshi.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
Ficción GeneralLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?