RAYUWA TA PRT 3 PG 4

12 2 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖

'''🅿️ART  3️⃣'''

*PAGE  4️⃣*

'''GIDAN HAJIA AMMIE.

Nadia ce zaune itada Ammie a parlour sai Nusaiba.

Nadia nasani nakuma fahimchi Halinda kike ciki a yanzu.

Amman karki damu bazan taba aura miki wanda bakyaso ba.

Kinaji yanzu kifadamin shin wa kikeso a cikin Lateef da Aslam?

Nadia Kallan Ammie tayi cike da hawaye a fuskarta.

Ammie Bansani Ba....
Domin bawanda zan iya juyawa baya a cikinsu.

Ammie Lateef yayimin komai a rayuwa ta Nida Mahaifina, haka Aslam don shine ma nake raye haryanzu.

Ammie bansani ba, bansan wanda nakeso ba....

Kinga Ya isa Nadia shikenan, Zan rabu dake yanzu harzuwa lokacinda zaki kara fuskantar kowanne daga cikinsu.

Zan kara baki wata damar domin keda kanki kigane wanda yafi cancanta dake.

Nadia ki nutsu kuma ki kwantar da hankalinki babu wani abinda zai faru.

Zan bar magana har zuwa lokacinda zaki kare karatunki baki daya nasan kafin wannan lokacin kinsan wanda yafi dacewa dake.

Nadia Kallan Ammie tayi domin kuwa ita gaba daya a rikice take.

Nagode Ammie, Nagode sosai da sosai da irin kaunar da kike gwadamin.

Karki damu Nadia Wannan nauyi nane kinjiko Saboda haka bawani abu bane.

Ammie ce kamar yadda ta saba ta mikama Su Nadia Kudi.

Nusaiba har zataki karba Ammie wani kallo tayi mata tadanyi yakenta sannan tace mungode Ammie.

Zansa Mustapha ya maidaku gida yanzu.

Zara'u Ammie tayi kira inda tace kiramin Mustapha.

Thom Ammie, fadar Zara'u.

Mustapha ne ya shigo,
Gasu Nadia nan ka kaisu gida kajiko.

Sannan idan kadawo kabiya ta wajen sakon nan.

Ammie ce ta dauki wayar ta Inda tace Mungama kuna iya zuwa sannan ta kashe.

Fitowa Su Nadia Sukayi Suka shiga Mota Domin a kaisu Gida.

GIDAN ALHAJI ABDULLAHI.

Mahaifiyar Aslam ce zaune itada Mahaifin Aslam din.

Toh yanzu Alhaji mene Abinyi?

Nima bazance ga abinyi ba har sai abinda Ammie tace tukunnah.

Amman ta wani bangaren nima naji dadin dawowar Nadia hayyacinta.

Sannan kisani fa daowawar Nadia hayyacinta ba hakan yana nufin kuma ta manta da Aslam bane.

Tana Sane dashi,

Amman kana ganin yanzu Dukda ta dawo hayyacinta zata yarda ta auri Aslam din?

Nima bansani ba, Amman Dai nasan tana sansa.

Amman banida tabbacin shine wanda zatace tanaso.

Yanzu haka Ammie tayi kiransu duka domin suyi magana ya kirani yacemin gashi a gidan nata.

Tohh, Allah ya bada Sa'a dai Amman yaron nan yadda ya kwallafa ransa akan Nadia ai idan bai aureta ba zai sami matsala.

Hmm karki damu a matsayinmu na iyayensa Mutayashi da Addua yadda koda bai sametan ba ba bazaiji babu dadi ba sosai.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now