RAYUWA TA PRT 2 PAGE 8

6 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL ✍🏽📔*

✨ _PART  2_ ✨

8️⃣

'''SHOPPING MALL.

Karfa kifadama Daddy cewar munzo nan don kinsan yace bai yadda kin samu Lafia ba saboda haka karki dinga fitowa.

Murmushi Nadia kawai tayi Masa da cewa Shikenan ai dama bazai sani ba.

Shiga ciki sukayi suna sayayyar su cikin farin ciki.

Ni dai a yaune na tabbatar da cewar Nadia da Aslam sun dace matuka.

Saidai Anya Aslam zai sami Nadia kuwa? Hmmm

POLICE STATION.

Ammie ce zaune kankujera Abdul Lateef yana Tsaye dasu Khaleed.

Hajia Mun tambayeshi amman yace baisan komai ba.

Munmatsashi sosai karshema nuna mana yayi baisan batarta ba, kuma shima yaji haushin hakan sosai.

Dpo kuna ganin da gaskia a cikin lamarin yaran nan kuwa?

Hajia kai tsaye bazamu mutum bashida laifi ba saidai a duk inda mai laifi yake Dan Sanda yakan iya ganeshi.

Kuma yace wannan mai laifi ne.

Muntambayeshi ina yake tsawon wannan watanni yace mana yana neman aiki ne.

Jami'an mu na kan hanya kuma sunkamashi ne zaibar gari.

Hakan yasa koda bashine ya sace Nadia ba toh lallai yanada wani kudiri nasa.

Wanda yakeson cimma akanta, dubada kalamansa da yakeyi.

Kodai yana cikin fushi da itane saboda tace bata sonsa kuma bazata aureshi ba.

Hakane! Inji Ammie.

Toh Amman Hajia Babu damuwa kuma bazamu turashi kotu ba saboda bamuda Isashshun hujjoji.

Zamu cigaba da Ajiyeshi har Allah yasa musami hujjoji masu kyau wanda zamu turashi kotu dasu gaba daya.

Dpo ya fada.

Toh Alhamdulillah! Hakanma yayi Dpo Mungode kwarai da gaske.

Haba Hajia Ai babu damuwa jin dadi nane kasancewa akan wannan case din.

Duba da cewa Yarinyar kinada Alaqa da ita.

Hakane Dpo Yarinyar Sirika tace Amman bansan acikin jikokina wane zai aureta ba.

Ko sanar da gidansu bamuyi ba halin da ake ciki saboda bamaso hankalinsu ya tashi.

Eh Hakane! Duk halin da ake ciki inshaAllah zan sanar da Abdul ya sanar dake.

Shikenan Dpo Nagode sai Anjiman.

Muje ko Abdul Lateef?

Thom Ammie kije Mota Ganinan..

Ammie fita tayi inda su Khaleed sukabi bayanta.

Dpo zan iya ganin shi wannan wanda ake zargin Lateef ya Tambaya?

Ehh Babu damuwa Muje ka ganshi mana.

Fitowa Sukayi, Kai kufitomin da Abu Adam daga Cell.

Yess Sir! Cewar Constable.

Fito dashi Akayi inda Yaga Lateef,
Tinaninsa Lateef ne yasa aka kamashi.

Sannunka?

Shiru Abu Adam yayi baiceda Lateef komai ba.

Kaga Abu Adam idan kaine ka dauke Nadia kawai ka sanar dani.

Zan taimakeka ka fita daga nan banason acigaba da ajiyeka anan.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now