RAYUWA TA PRT 3 PG 6

10 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖

'''🅿️ART  3️⃣'''

*PAGE  6️⃣*

'''GIDAN ALHAJI MUBARAK.

Lateef ne gaban Mota shida Salman.

Sarah ce tafito cikin wata Doguwar riga Sky Blue mai tsananin kyau.

Kushigo Mana Salman fadin Sarah.

Lateef duk shidai kunya yakeji, fitowa yayi daga cikin motar shida Salman din.

Sarah ta wuce gaba ta kaisu Parlourn Baki na gidan.

Suka zauna.

Nayi mamaki da kacemin zakuzo Salman.
Amman ina fatan lafia babu wata matsala koh?

Hmm Sarah kenan Lafia lau Nida mutuminne baki ganshi bane?

Sarah wani irin kallo tayima Lateef din mai shiga rai da murmushi.

Da a india muke nasan har wani taken soyayya za'a sako!

Lateef kasa hada ido yayi da ita.

Naganshi Bayan ma ni yaki kulani sarah ta fadi.

Kaga ka bude baki kayi magana malam Munzo kuma kayi shiru kakasa cewa komai.

Shikenan Bari Abbah na yana sama bari nace kunzo saiku gaisa koh?

A ah dakata Sarah ba saikin kirah shi ba Ni kece nazo muyi magana dake... Lateef yace.

Kaga Kaifa bada Sarah kuka sami matsalar kaba da mahaifin tane kabari ta kirashi ya sauko mugaisa saikace hakuri kazo ka bashi dama.

Sarah murmushi tayi sannan tace hakane Lateef ni banida matsala kugama da Abbah kawai.

Kinga jeki sanar dashi kinji inji Salman.

Sarah tashi tayi ta hau sama don sanar da mahaifinta.

Amman ya zakace taje  ta sanar dashi yanzu me zance Salman.

Kasan abinda ya faru a baya fa ni gaskia banason Haduwa dashi yanzu.

Kaga ka kwantar da hankalin ka Malam Abdul.

Zai fahimceka inshaAllah kajiko.

Sarah ce ta sauko tace gashi nan dama fitowa zaiyi ya shirya.

Bakusha drinks din ba.

Hmm zamusha ai fadar Salman.

Mahaifin Sarah ne yake saukowa daga Sama.

Da kanshin turarensa ya mamaye Parlourn gaba daya.

Saukowa yayi ya matso kusa dasu sannan suka hada ido da Abdul Lateef.

Cikin fada da bacin rai yace MEYA KAWO WANNAN GIDA NA!!?

Sarah bakida Hankali me wannan Yaron yakeyi a nan gidan?

Abbah Abdul Lateef ne,

Tambayar ki nakeyi ubanme ya kawoshi gidana?

Wallahi Sainaci miki mutunchi,
Kaikuma mekazoyi nan?

Meyakawo ka Gidan nan?

Meya ka woka wajen yarinyar da  bakaso.?

Toh bari kaji na fada maka Abdul kake kowa?

Wallahi kaida Sarah saidai kallo, dan idan duk mazan duniya zasu kare bazan taba aura maka 'yata ba.

Sannan ka tattara kayayyakin ka gaba daya kabar gidan nan kafin nayi maka cin mutunchin da yafi wannan.

Shiru Lateef yayi baice komai.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now