*RAYUWA TA THE NOVEL*✍🏽📔
_Page 5_
'''WASHE GARI.
GIDAN SU NADIA.
Ikon Allah! Yanzu sai yaushe zaka dawo? Nadia ce take Tambayar Lateef.
Dayake babu tafiar a cikin plan dina nima, bazan dade ba gaskia zanyi Like 2weeks haka.
Nadia Girgida kanta kawai tayi tareda cewa 2weeks ai zaka dade,
Hmmm Karki damu, Malama Nadia. Kodanke bazanje nayi zamana ba.
Da ace akwai wani Namijin bani ba a gidama shine zaije.
Toh Saini din dole.Nadia kam alamunta batason Yatafin, kawai cewa tayi Shikenan.
Allah ya kaika lafia ya dawo da kai lafia.Ameen ameen.
Yauwa Nagama komai a harkar makarantar ki, jiya da daddare, Ehmm Private University ce.
DIAMOND UNIVERSITY (DU)!!!
Amman Malam Abdul Lateef makarantar nada Tsada fa meyasa ita? Nadia ta tambaya.
Nafiki sanin tanada Tsada Malama Nadia, kema ai ba Arha bane dake da za'a saki a makaranta me Arha.
Kinga Nagama Komai Ehmm Tafiya na Gobene inshaAllah, Ke Kuma Anjima Zamuje Inkaiki.
Screening da Saura Interviews haka kinjiko.
Baba Yana Ciki ne?
Ehh Baba Yana ciki,
Kaini In dubashi! Fadar Lateef.Cikin Suka Shiga Bayan Sunyi Sallama,
Nadia ce tashiga domin sanar da mahaifinta.Kashigo Mana yana Parlour ma,
Assalamu Alaikum, Lateef yayi Sallama.
Baba Ina Wuni.Lafia lau Malam Abdul,
Ya Saukin Jikin Kuma?
Jiki Alhamdulillahi, jiki ai yayi karfi.
Tohh Masha Allah, Haka akeso aiBaba Dama Wata Tafiya ce ta tasomin, Amm Mahaifina ne ya turani domin zuwa wani meeting.
Kuma Ba'a kasar nan bane, Toh dama dayake nagama duk wani abu da ake bukata a makarantar da Nadia zata fara zuwa.
Nace duka bari nasar da kai, akwai Sauran abubuwa wanda dole sai taje da kanta.
Shine nace banaso ta kara fita ita kadai din nan tana neman abin hawa banaso gaskia.
Nace idan ta shirya koda zuwa anjima ne saina dawo in kaita kawai.
Tohh!! Malam Abdul, Naji batuka
Ahh Allah ubangiji ya kiyaye hanya ya yatsare.Allah kuma ya bada abinda za'aje nema.
Ameen ameen Baba,
Sannan Maganar Makaranta Duk Abinda kaga ya dace ayishi domin kaga ni ba ilimin abin bane dani.
Inyaso saikuje gaba daya akwai Kawarta Nusaiba duka saikuje.
Thomm! Babu Damuwa Baba Nagode da wannan Dama daka bani.
Allah Ya saka da Alkhairy,
Haba malam Abdul ai wannan Ba wani abu bane.Mune zamuyi maka Godia, Allah Ya Tsareka.
Ameen ameen Baba.Lateef Tashi yayi yafito shida Nadia.
Wallahi Malam Abdul Lateef nibansan wane irin kalamai zandinga amfani dasu wajen gode maka ba.
Allah Ubangiji ya saka maka da Alkhairy, Allah ne kadai zai biyaka danni bazan iya biyan kaba.
Hmmm Malama Nadia kenan! Karki damu kinji Bawani abu bane idanna yi miki duka wannan.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
Ficção GeralLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?