RAYUWA TA PRT 3 PG 11

10 0 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖

'''🅿️ART  3️⃣'''

*PAGE  1️⃣1️⃣*

'''GIDAN ALHAJI MUMIN.

Amman meyasa kuka batama Ammie rai kaidashi din?

Meyasa bakuji maganar taba kukayi abinda kukayi?

Mahaifin Khaleed ne yakema Khaleed din fada.

Haba Daddy, Lateef lokaci yayi da zai san ba tsoron sa mukeyi ba.

Yana yaudarar yarinya kuma ace mu munsani bazamu bi mata haqqin taba.

To masu bin haqqi, yanzu garin bin haqqi ga abinda kukaja dukan ku yanzu tace babu ku babu Nadia.

Daddy shiyasa nazo gareka Dan Allah kasameta kuyi maganah.

Kace mata bazamu karaba,

Khaleed kunyi kuskure, domin ni kaina ba lallai Ammie ta saurareni ba.

Amman zanje Zamuyi magana.

Yauwa Daddy dan Allah!

DIAMOND UNIVERSITY.

Nadia ce cikin Libarary tana karatu.
Nusaiba shigowa tayi tace sai nemanki nakeyi mekikeyi Anan kuma?

Mezanyi a ajin idan banzo nan ba Nusaiba ko so kike na tsaya nima nayita surutun da bashida Amfani.

Shikenan Ba wannan ba An samu An raba Mana test, Naki Very Poor Sanadiyar baki shigowa Lectures dinsa.

Bakida Attendance Nadia kinfara wasa fa.

Nusaiba wallahi karatun nan yanzu kawai ina yin sane.

Hmmm kedai wasa nakeyi miki, Kinsan wani Abin mamaki kuwa?

Nadia Bakya shiga Class Amman an raba test kece highest ke kadai kikeda 29/30

Sauran 26 below ne.

Alhamdulillah! Tana ina Muga abinda nayi?

Yace bazai bani ba saidai kije ki karba da kanki yana Office dinsa bai yadda kece kikayi ba.

Hmm Mal. Mannir yacika rigima Shikenan bari naje na Amso koh.

Nadia sauko tayi sannan ta nufi Staff block.

Malam. Mannir ne zaune kan kujerar sa Yana Marking Tests.

Assalamu Alaikum,

Wa'alaikumu Assalam Shigo cewar Malam Mannir.

Sir nice Nadia Ahmad Test dina na wajenka kace nazo na karba.

Ok! Yess Kece kenan?

Eh Sir nice.

Tasowa Malam mannir yayi yace kifadamin gaskia ina kika saci amsa.

Sir ban saci amsa ba, karatu nayi.

Ke rufemin baki dallah karatun banza kece kadai kike karatun sauran Dalibai da suke karatun meyasa basuci haka ba?

Sir, wallahi bansaci Amsa ba.

Shikenan Nadia muyi abu guda daya,
Idan har na sanarwa da makaranta abinda kikayi toh fa kin lalata Karatun kine.

Saboda zasu koreki ne hade da cin ki tara mai yawa.

Idanma kuma basu kamaki ba.

Kinaji Nadia tinda naga a waye kike kuma bazamu tsaya wani cece kuce ba.

Kibani Kanki Nikuma zan rufa miki Asiri zan kuma kara miki wani Marking a lokacin jarabawa.

Nadia Wani Daram Dam dam!!! Taji a zuciyarta.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now